Gidauniyar Zakah da Wakafi a Jihar Gombe ta shirya buda-baki tare da marayu domin faranta musu rai a gidan marayu da ke unguwar Tumfure a fadar jihar.
A buda-bakin na musamman da aka yi tare da iyalan jami’an gidauniya, an soya wa marayun kaji an dafa musu shinkafa da shayi, ga kuma ‘ya’yan itatuwa, alfarmar watan Ramadan.
- An yi garkuwa da direban ofishin Mataimakin Gwamnan Nasarawa
- Mai PoS ya shiga hannu kan kashe N280m da aka tura masa bisa kuskure
A yayin ziyarar ‘ya’yan jami’an gidauniyar da suka sha ruwa da marayun sun yi ta wasa tare suna hira da juna bayan shan ruwan.
Shan ruwan ya samu halartar manyan jami’an gidauniyar, ciki har da shugabanta, Dokta Abdullahi Abubakar Lamido, da iyalansu da sauran su.
Shugaban gidauniyar, ya ce makasudin ziyarar shan ruwa da marayun shi ne domin tuna musu cewa wata rana wasu mutane irin hakan za su kula da su a rayuwa kuma za a samu masu taimaka musu a cikin su.
Dokta Lamido, ya ce an kafa gidauniyar ne dan raba zakka da wakafi da kuma taimaka wa marasa galihu da ke cikin al’umma ta kowacce hanya.
Daga nan sai ya yi kira ga masu hannu da shuni da su hada kai da gidauniyar wajen taimaka wa marayu da kuma aike wa da zakkarsu inda ta dace idan suka fitar.