✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniyar MacArthur za ta bai wa jami’ar ABU gudunmuwar $15m

Babu wata kungiya a ciki da wajen Najeriya da ke ta tallafa wa jami'ar kamar gidauniyar MacArthur.

Gidauniyar MacArthur za ta bai wa Jami’ar Ahmadu Bello gudunmuwar dala miliyan 15 domin bunkasa harkokin karatu da bincike.

Shugaban gidauniyar, Dokta Kole shettima ya ce gidauniyar za ta bai wa jami’ar gudunmuwar a wani yunkuri na ci gaban kasa.

Dokta Kole ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da kasida a wurin bukin cika 60 da kafa jami’ar ta Ahmadu Bello da aka gudanar a Jami’ar dake Zariya.

Ya ce wasu daka cikin gudunmuwar sun hada da hade Asibitin Koyarwa na jami’ar da ke Shika da rassan jami’ar na Samaru Kongo da na’urar yanar gizo.

Ya kara da cewa gidauniyar ta tallafawa dalibai masu karatun digiri na 3 su 67 da masu yin digiri na 2 su 87 a jami’ar.

Dokta Kole ya roki gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su kara yawan kudin da aka warewa bangaren manyan makarantun kasar nan.

Ya yi bayanin cewa hakan zai tabbatar da gudanar da aiki yadda ya kamata a bangaren kuma ya magance yawan lamarin kaura da malaman jami’a ke yi.

Haka kuma Shettima ya shawarci tsoffin daliban jami’ar da su agaza wa kokarin da gwamnati ke wajen magance matsalolin da jami’ar take fuskanta.

A nasa jawabin, Shugaban jami’ar, Farfesa Kabir Bala ya nuna farin cikinsa bisa dangantakar da ke tsakanin jami’ar da gidauniyar MacArthur.

Farfesa Bala ya bayyana cewa baya ga Asusun Kula da Manyan Makarantu na Kasa, watau TETFUND babu wani mahaluki ko wata kungiya daga ciki da wajen Najeriya da ke ta tallafa wa jami’ar kamar gidauniyar MacArthur.

Ya ce jami’ar ba za ta mance da Daraktar gidauniyar ba bisa tallafin kayan sadarwa da zamanantar da dakunan karatu da kuma kafa wasu cibiyoyi.

Farfesa Bala ya ce daga cikin cibiyoyi da suka ci moriyar gudunmawar sun hada da cibiyar bunkasa sadarwa da bunkasa yankunan karkara da cibiyar bunkasa lafiyar dabbobi da dai sauran su.

Shugaban jami’ar ya ce an kafa jami’ar ce a shekarar 1962 kuma a shekarar 2022 ya kamata a gudanar da bikin cika shekaru 60 amma saboda yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ya sa ba a yi bikin ba sai a wannan shekarar.

Shi ma a nashi jawabin, shugaban taron, Madakin Zazzau, Alhaji Munir Ja’afaru ya bukaci gwamnati ta bai wa manyan makarantu fifiko kasancewar ilimi shi ne ginshikin ci gaban kasa.

Ya kara da cewa hakkin kowa ne a ga cewa manyan makarantun kasar nan suna samun kudi domin su bunkasa.

Munir Ja’afaru ya kuma bukaci tsoffin daliban jami’ar ta Ahmadu Bello da su rika taimakawa kasancewar jami’ar ta zama kaddara ta kasa da baikamata a bari ta ruguje ba.