Gidauniyar Daily Trust tare da haɗin guiwar Gidauniyar McArthur ta shirya wa ’yan jarida daga sassan Najeriya horo na kwana uku kan yadda ake binciken ƙwaƙwaf a Jihar Kaduna.
Yayin buɗe taron horon, Mukaddashin Shugaban Gidauniyar Daily Trust, Malam Bilya Bala, ya bai wa mahalarta shawarar su ƙara dagewa a ɓangaren binciken ƙwaƙwaf domin su bambanta da sauran gama garin ’yan jarida masu yin rahotannin yau da kullum.
- Ngozi Iweala ta sake zama Shugabar Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya
- NAHCON ta mayar wa alhazai N5.3bn kan matsalolin Hajjin 2023
Bala ya ƙara da cewa, “Kowa zai iya shiga kafofin sada zumunta ya wallafa abin da ya ga dama, amma idan aka yi maganar binciken ƙwaƙwaf, wannna wani abu ne na daban.
“Yana buƙatar lokaci da kuɗi da kuma ƙwarewa, shi ya sa muka mayar da hankali wajen bayar da horo na musamman kan irin wannan aikin,” in ji shi.
Kazalika, ya bayyana irin yadda binciken ƙwaƙwaf yake da tasiri a tsakanin al’umma da yadda yake sawa mahukunta su ɗauki matakan da suka dace.
Shugaban Daraktan Shirye-shirye na Gidauniyar, Mista Theophilus Abbah, a yayin bikin ya bai wa mahalarta horon shawarar su jajirce waje binciko da yaɗa labaran gaskiya ta hanyar cire tsoro da binciken ƙwaƙwaf.
Ya ce, “Ɗan jarida mai binciken ƙwaƙwaf ya kan bayyana abin da waɗansu ke ɓoyewa ne, don haka dole ne ya zama yana da hujjoji masu ƙarfi domin tabbatar da abin da ya binciko.
“A wasu lokuta irin wannan binciken yana da tsoratarwa, amma dole ɗan jarida ya zama mai dabara wajen ɓoye kansa domin bayyana ɓarna.”
Har ila yau, Mista Abbah, ya ce an shirya horon ne domin inganta aikin jarida da ƙara ƙarfafa ɓangaren binciken ƙwaƙwaf ta hanyar amfani da sahihan bidiyo, sauti da hotuna.
Horon wanda ya gudana a Kaduna, ya haɗa ’yan jarida daga gidajen talabijin da rediyo da jaridu da kuma kafafen yaɗa labaru na zamani daga sassan Najeriya.
Bayan kammala horon, Gidauniyar ta raba wa ’yan jaridar da suka samu horon takardar shaidar samun horo a kan binciken ƙwaƙwaf.