A farkon makon nan ne Gidauniyar Daily Trust tare da hadin gwiwar Gidauniyar MacAuthur ta fara horar da ’yan jarida sanin makamar aiki a kan binciken diddigi a kan Kasafin Kudin kasa.
An shirya taron bitar na kwanaki uku ne a Jihar Kano domin ‘yan jaridu daga jihohi daban-daban da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
- Yadda bolar bayan gidan sarki take jefa Kanawa a cikin kunci
- Jonathan ya taya Tinubu da Atiku murnar zama ’yan takara
Wakiliyarmu wadda ta halarci bitar ta ruwaito cewa an horar da ‘yan jaridu guda 30 kan binciken yadda gwamnati ke kashe kudaden al’umma da ke baitul mali, da kuma bibiyar kasafin kudi, domin tabbatar da gwamnatoci sun sauke nauyin da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya dora mu su.
Da yake jawabi yayin bude taron Shugaban Gidauniyar Daily Trust, Bilya Bala ya ce horas da ‘yan jaridun na daga cikin muradansu na inganta aikin jarida a Najeriya.
Ya ce: “Abin damuwa ne abubuwan da muka gani a wasu ‘yan shekaru da suka gabata, mun hadu da ‘yan jaridun da ba su taba halartar kiwocce bita ba tun da suka kammala karatunsu na jami’a fiye da shekaru 10.”
“Abin tashin hankali ne musamman idan muka yi la’akari da ci gaban da ake samu a bangaren a duniya, amma kusan duk haka abin yake a kafafen yada labaran kasar nan.
“Shi ya sa muka yunkuro domin kawo sauyi, shi ya sa muka tattaro wadannan ‘yan jaridun muke ba su horo tun daga tushe,” in ji shi.
“A hannu guda kuma bibiyar kasafin kudi, abu ne mai matukar muhimmanci domin tabbatar da gwamnatocinmu sun yi abinda muka zabe su yi mana, kuma a yi shi a bude ba tare da wata rufa-rufa ba.”
Haka kuma Shugaban Gidauniyar ya ce “Mun sha ganin yadda ‘yan jarida suka bankado badakaloli na ayyukan gwamnatin tarayya, ministoci, da ma shugabannin ma’aikatu, musamman ma kan cin hanci da rashawa, almubazzaranci, da son zuciya.”.
Bala ya kuma ya ce wannan badakala na karuwa ne sakamakon ‘yan jarida ba sa aikin da Kundin Tsarin Mulki ya basu damar aiwatarwa. Don haka wannan horo ya na fatan ya zamo mabudin ido ga ‘yan jaridar.
A nasa bangaren Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano Malam Muhammad Garba, wanda Darakatan Ma’aikatar Inuwa Yakasai ya wakilta, ya mika godiya ga cibiyar da ma wadanda suka shirya bitar wadanda a koda yaushe ke kokarin ganin an aiwatar da abubuwa da kwarewa.
Haka zalika ya ce horon ya zo a alokacin da ya dace kasancewar lamura da dana ba sa tafiya yadda ya kamata, kuma hakkin ‘yan jarida ne su fito da su duniya ta sani.
“Don haka ya zamo dole mu yi yaki da son zuciya a yin hakan, domin hakan ne abinda zai ceto kasarmu”, in ji shi.
Ya kuma tabbatarwa da cibiyar cewa gwannati a shirye take ta ci gaba da ba da hadin gwiwa domin ganin an cimma hakan,” in ji Daraktan.
Sauran wadanda suka ba da horo a bitar sun hada da tsohon Kwamishinan Kudi na Jihar Kano Farfesa Kabiru Isa Dandago, da Daraktan Gidauniyar Daily Trust, Theophilus Abbah, Caheles Mba daga cCbiyar Dataphyte, sai Atiku Samuel daga Cibiyar Hadaka kan Kasafin Kudi ta Kasa da Kasa.