✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniya ta tallafa wa wadanda rikicin kabilanci ya shafa a Gombe

Mutum daya ya rasa ransa a rikicin da ya auku a tsakanin ’yan kabilar Waja da Lunguda.

Gidauniyar SNAP Care Foundation da ke gudanar da ayyukan jin kai a fadin kasar nan ta tallafa wa al’ummar kabilar Lunguda da Waja wadanda rikicin kabilanci ya shafa a Karamar Hukumar Balanga ta Jihar Gombe

Aminiya ta ruwaito cewa, an yi wani mummunan rikicin kabilanci a tsakanin ranakun 8 da 9 ga watan Fabarairu na wannan shekarar, inda ’yan kabilar Waja suka farwa kabilar Lunguda a kauyen Nyuwar suka kone musu gidaje da kayan abinci har ta kai ga ran wani mutum guda ya salwanta.

A yayin mika kayayyakin tallafin a garin Nyuwar, Bala Wala Alhaji Muhammad Danjuma Muhammad wanda Sarkin Malaman Waja, Alhaji Abdullahi Gombi ya wakilta, ya mika godiyar sa matuka ga wannan kungiya ta SNAP Care bisa tallafin da suka kawo musu a lokacin da rikicin ya faru a tsakanin ’yan kabilar ta Lunguda da Waja.

Bala Waja, ya bayyana Gidauniyar SNAP Care a matsayin kungiya mai tausayin jama’a da hakan ya sa ta jin kansu har ta kawo musu wannan tallafi a lokacin da suke bukata.

Ya ja hankalin kabilun biyu na Waja da Lunguda da cewa su kaunaci juna su zauna lafiya, yana mai cewa bai kamata a rika yawan samun tashe-tashen hankula a tsakaninsu har ta kai ga rasa rai ba.

A jawaban  da suka yi, Hakiman Nyuwar da Jessu, Mista James Pisaghi da Misat Laban Maina, sun yi godiya ga Allah Madaukakin Sarkin bisa wannan kayan tallafi da Gidauniyar SNAP Care ta kawo musu, inda suka ce tallafin ya zo a lokacin da suke da bukatarsa

A nasa tsokacin, Shugaban al’ummar Nyuwar na Kasa, Mista Galiyus S Zulum, ya yi godiya a kan kokarin wannan gidauniyar bisa tausayawa al’ummar su da ta yi har ta kawo musu dauki.

Zaliyus ya roki gwamnati da ta kafa wamitin bincike domin gano masabbabin faruwar wannan rikici da masu hannu a ciki domin a hukunta su.

Kazalika, ya roki da a kafa wani kwamitin da zai nazari kan irin asarar da mutanen su suka yi domin ganin yadda za’a rage musu radadinta.