✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidan Badamasi: Za a fara haska zango na 3

Bayan daukar lokaci ana daukar zango na 3, an sanar da ranar da za a ci gaba da haska shirin.

Wasan Kwaikwayon barkwancin mai suna ‘Gidan Badamasi’ Zango na 3 zai ci gaba a ranar 7 ga Afrilun 2021.

Sanarwar ta fito ne daga shafin twitter na Labaran Kannywood.

Tun da farko tashar Arewa24 ta haska zango na daya da na biyu na shirin.

Yanzu kuma bayan kammala daukar zango na uku, an sanar da ranar za a ci gaba da haska shi a tashar.

Nazir Adam Salih ne ya tsara labarin, Falalu Doyari kuma ya shirya, Nasiru Ali Koki da Muhd M. I. Sardauna suka ba da umarni.

’Yan wasan sun hada da; Falalu Dorayi, Magaji Mijinyawa, Mustapha Naburaska, Umma Shehu, Hauwa Ayawa, Nura Dandolo, Ado Gwanja, Tijjani Asase, Hadiza Kabara, Aminu Mirror da sauransu.