Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja ta kubuto almajirai 15 daga hannun masu azabtarwa da bautar da yara a garin Suleja na jihar Neja.
Cibiyar, kamar yadda aka sanar da Aminiya tana azabtar da yara kanana ne masu shekaru biyu zuwa sama a Angwa Kwamba da ke Suleja.
Ya sanda sun ce, da suka kai samame gidan sun tarar da yawancin almajiran da raunika da tabbai iri-iri a gadon bayansu sakamakon azabtarwar da suka fuskanta.
Kakakin rundunar, ASP Wasiu Abiodun, ya ce sun gudanar da samamen ne bayan samun bayanan sirri da suka samu.
Ya ce, lokacin samamen sun kamo wani dan shekara 46, bisa zargin laifin azabtar da kananan yara 15 da cin zarafinsu da sunan almajiranci.
Ya kuma ce sun samu abubuwa kamar marin kafa da sarkoki da ake amfani da su wajen daure yaran a cikin gidan.
Ya ce rundunar ta damka yaran a hannun hukuma mai kula da hakkokin yara ta jihar, kuma za su kai masu laifin kotu da zaran sun kammala binciken su.