✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Giba da illolinta (1)

Daga hudubar Sheikh Salihu bin Abdullah bin Humaid, Masallacin Harami na Ka’aba, Makka Fassarar Salihu Makera Huduba ta farko Godiya ta tabbata ga Allah, muna…

Daga hudubar Sheikh Salihu bin Abdullah bin Humaid,

Masallacin Harami na Ka’aba, Makka

Fassarar Salihu Makera

Huduba ta farko

Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman gafararSa muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu, wanda Allah Ya shiryar babu mai batar da shi, wanda kuma Ya batar babu mai shiryar da shi. Mun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Ya da abokin tarayya, a gare Shi, kuma mun shaida lallai Shugabanmu Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa. Allah Ya kara tsira da amince a gare shi da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa.

Bayan haka, ina yi mana wasiyya da bin Allah da takawa, wanda ya yi maSa takawa Ya isar masa, wanda ya ji tsoron mutane ba su isar masa. Ina yi mana wasiyya da takawa, wadda ba Allah Ya karbar waninta, kuma ba Ya jinkan kowa sai ma’abutanta, ba Ya bayar da lada sai a kanta, masu wa’aztuwa da ita suna da yawa, amma masu aiki da ita kalilan ne, Allah Ya sanya mu cikin masu takawa.

Ya ku Musulmi! Addinin Allah ya cika ya kammala, ya kunshi akida da shari’a da tauhidi da ibada da mu’amala da dabi’u, yana zance da hankali da zuciya da jiki da rai a cikin al’amuran da suka shafi shari’a da halaye da tarbiyya, addini daga Ubangijinmu yana tsara dokoki da rayuwa ga Musulmi mai mutunci da tsarki na zahiri da badini. Ya zamo Musulmi mai kubutacciyar zuciya, mai kame harshe, mai da’a ga Ubangijinsa mai halin kirki ga jama’a. Mai kokarin tsare mutuncinsa da kin bin son rai. “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku nisanci abu mai yawa na zato. Lallai sashen zato zunubi ne. Kuma kada ku yi rahoto, (bincikar laifin mutane).” (K: 49:12).

Musulunci addini ne na gaskiya da hukunce- hukuncen addini suke ta’allaka da shi tare da tsarkake zukata, al’amura su rika gudana bisa ma’aunin gargadi. Addini ne da ke rainon jama’a masu addini da gudun abin da aka haramta, masu kamewa daga giba da halartar wurin da ake gibar, ba su yin mummunan zato ga kowa, kuma ba su neman bankado al’aurorin (sirrin) mutane.

Ya ku ’yan uwa! Daya daga cikin dabi’un da wannan addini ya tsayu wajen yakarsa, yaki na sosai saboda illarsa a tsakanin jama’a kuma yake bata al’amura da jawo rashin mutunci da raunana addini da zubar da mutuncin mutane, kuma daya daga cikin manyan kaba’irai, masu jawo ukuba, da mai aikata su ko mai yarda da su da mai saurarensu suke da zunubi, shi ne, giba, wato ka ambaci laifin mutum a bayansa, ko ka ambaci dan uwanka da abin da ba ya so, ya alla yana da wannan abin da ka fada ko a’a. Haka Manzonmu Muhammad (SAW) ya bayyana.

Ubanjinku Yana cewa: “Kuma kada sashenku ya yi gibar sashe. Shin dayanku yana son ya ci naman dan uwansa yana matacce? To, ku ki shi (cin naman). Kuma ku bi Allah da takawa. Lallai Allah Mai karbar tuba ne, Mai jin kai.” (K:49:12).

Ya ku Musulmi! Lallai jininku da dukiyarku da mutuncinku haramun ne a tsakaninku. Giba tana da sunaye uku cikin Littafin Allah Madaukaki, wato giba da kage da kirkirar karya. Idan abin da aka fada a kan mutum daidai ne, shi ne giba, idan kuma ka fadi abin da ya zo maka wato abin da ka ji, to ya zama kage, idan kuma ba haka lamarin yake ba, to ya zama keren karya, haka ma’abuta ilimi suka bayyana. Giba ta kunshi duk abin da yake nufin batunci ga wani, ya alla ta magana ko yafuce ko zunde ko a rubuce, domin alkalami shi ma harce ne.

Giba tana iya zama ta hanyar nakasa mutum saboda addininsa ko halinsa ko dabi’arsa ko dangantakarsa ko nasabarsa, kuma duk wanda ya aibata sana’a babu shakka ya aibata ma’abucinta ne.

Ku saurari yadda Annabinku Muhammad (SAW), yake kiran wadanda aka jarabtu da wannan cuta mai halakarwa: “Ya wanda ya yi imani da harcensa, amma imani bai shiga zuciyarsa ba! Kada ku yi gibar Musulmi, kada ku bi al’aurorinsu, domin duk wanda ya bi al’aurar dan uwansa, Allah zai bi al’aurarsa, wanda kuwa Allah Ya bi al’aurarsa, zai kunyata shi koda a tsakiyar gidansa ne.”

Alhassan (Allah Ya yi masa rahama) ya ce, “Wallahi giba ta fi saurin cinye addinin mutum fiye da yadda tsutsa ke cin naman mutumin da ya mutu.”

Ka ji mamakin mutumin da ke jingina kansa da ma’abuta gaskiya, ta yaya zai rika yin giba, alhali ya san wanda aka jarabce shi da giba yana da karkatacciya kuma bakar zuciya wadda ta ginu a kan kin mutane da kin alheri. Ba ya damuwa da nasa laifin kamar yadda yake damuwa da cutar waninsa! Hutunsa da natsuwarsa su ne ya ga ni’ima ta gushe daga waninsa, burinsa kullum ya ga bala’i yana samun waninsa, abin da yake faranta masa rai ya ga dan uwansa bai samu wani alheri ba, ya ga masifa tana sauka masa a kai a kai! Fushinsa da bacin ransa ya ga alheri ya same ka, ko ka dace ko arziki ya zo maka cikin sauki, ko ya ga wani alheri yana biyowa ta hannunka. Shin dabi’ar mumini ne wannan? Shin mumini zai so cutar da dan uwansa kuma a ce ba ya son ’yan uwantakar imani ta darsu a zuciyarsa? “Shin dayanku na son ya ci naman dan uwansa ne yana matacce?” (K:49:12).

Ma’abucin giba mutum ne mai zakin baki, idonsa kuma a bushe yake, ba ya da imanin da zai hana shi yin giba, ba ya da muru’ar da za ta sa shi aikata kyawawan halaye. Idan ya samu abokin giba sai dabi’arsa ta koma kamar ta jahilai, ya yi ta sakin magana har ta kai ma’abuta imani su kosa da shi. Zai rika sakin baki a kan shugabanni da malamai da masu kima da ma’abuta matsayi, kai har ma a kan wawa da jahili a kowane wurin zama da wurin taro!

Magana a wajensa abar sha’awa ce, idan aka dora shi a kan sha’anin mutane ya bata al’amarin, idan zai yi magana a kan al’amarin addini da ilimi sai ya juya gaskiya har ya zubar da kimarsa. Zai yi ta surutu har mai hankali ya gane cewa ba ya da kaifin hankali ko dogon tunani. Mai yawan gardama ne, yana kutsawa da harcensa cikin addini da siyasa da ilimi da ladab da ada, wannan shi ne sababin tabarbarewar ilimi da bullowar sababbin mazhabobi da rarrabuwar kai a al’amuran addini da harkokin rayuwa! Wannan abin kaico ne a rika amfani da harce (da alkalami ko kafar sadarwar zamani) wajen jidali da jayayya da giba da keren karya da kage bayyananne.

Mai giba a duk inda ya zauna yakan bata lokacinsa ne wajen bin aibobin mutane da neman kura-kuransu, ba ya jin dadin komai, illa kutsawa cikin mutuncin mutane, mai zunde mai yafuce mai yada annamimanci. Bonensa! Sannan bonensa! Yana furta maganar da za ta jefa shi a wuta na tafiyar da ta fi nisan da ke tsakanin Gabas da Yamma.

Ya ku Musulmi! Mafi munin wannan da makamantanta da mutum ke aukawa a ciki, shi ne gibar shugabannin Musulmi da malamai da masu tsare doka da kula da kyautata tarbiyya, mutanen da suke umarni da gyara a tsakanin jama’a. Sai su rika kutsawa cikin mutuncin mutanen kirki masu kima, suna zubar da mutuncinsu da martabarsu suna sukarsu da bata su, suna sukar kyawawan ayyukansu, suna sanya shakku a kan matsayinsu da cancantarsu!

Ba za a ambaci wani babba ba, face sun nakasa shi, ko sun zage shi, ba za a bijiro da wani mutumin kirki ba, face sun tuhume shi, suna watsa karya da jirkita abubuwa game da shi, suna tuhumar amintattu suna auka wa salihai, suna tayar da fitina suna shuka gaba da kiyayya, suna yanke zumunta suna rarraba kan jama’a, suna rura wutar gaba, suna watsa mata man fetur, suna watsa tuhumomi iri-iri suna bin aibobin mutane, su ce wannan zololo ne, wancan dan dukwi ne, wannan jahili ne wancan fasiki ne, wannan mai kazar-kazar ne, wancan kuwa jirgin dankaro ne ko yana tafiyar da al’amura a sulo. Idanuwansu suna yafuce, harasansu suna zunde, wuraren zamansu sharri ne, zama da su cuta ce, aikinsu abin ki ne, maganganunsu ababen kyama ne!