A ranar Talatar da ta wuce ne kasar Ghana ta yi kaca-kaca da ta Masar a gasar neman gurbin zuwa cin kofin duniya. Wasan ya gudana ne a filin wasa na Ghana da ke Accra.
Kwallaye biyu da shahararren dan kwallon Ghana Asamaoh Gyan ya zura a ragar Masar da kuma wacce dan kwallon Masar Wael Gomma ya jefa a ragarsu da ta dan kwallon Ghana Waris da kuma ta Christian Atsu ne suka ba Ghana damar lallasa Masar da ci 6-1.
Mohammed Abou-Treka ne ya jefa wa Masar kwallo daya tilo a bugun daga kai sai mai tsaron gida (fanariti).
Kimanin shekara 30 kenan da wata kasa a Nahiyar Afirka ta doke Masar da kwallaye fiye da biyar a raga sai a wannan karo.
Yanzu Ghana za ta bi Masar gida ne a wasa zagaye na biyu a watan gobe idan Allah Ya kaimu.
Ghana ta yi watanda da kasar Masar
A ranar Talatar da ta wuce ne kasar Ghana ta yi kaca-kaca da ta Masar a gasar neman gurbin zuwa cin kofin duniya. Wasan ya…
