Getafe ta rike Real Madrid canjaras a wasan da aka tashi babu ci yayin karawarsu a mako na 32 a gasar La Liga da suka fafata daren Lahadi.
Rasa maki uku da Madrid ta yi a wasan ya nuna cewa babu tabbacin za ta ci gaba da zama a mataki na biyu a teburin gasar ta Sfaniya.
A yanzu haka, akwai tazarar maki uku tsakanin Real Madrid da Atletico Madrid wacce ta ci gaba da kasancewa a saman teburin gasar bayan ta lallasa Eibar da ci 5-0.
A yayin da a irin wannan kadami babu wani uzuri da ake yi wa manyan kungiyoyin kwallon kafa duba da yadda karshen kakar wasanni ta karato, sai dai wasu na ganin Real Madrid ba ta samu maki ukun da aka yi hasashe ba sakamakon yadda wasu manyan ’yan kwallonta ba su buga wasan ba.
Akwai manyan ’yan kwallon kungiyar da ke fama da jinya ta samun rauni yayin da wasunsu kuma sun killace kansu bayan kamuwa da cutar Coronavirus.
Yanzu haka dai Barcelona mai kwantan wasa, tana ta uku a teburin La Liga da maki 65, inda take da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid.