Shugaban Majalisar Wakilai, Mista Femi Gbajabiamila ya yi kira ga Hukumar Sadarwa ta Kasa wato (NCC) ta tabbatar kowane layi an yi rajistarsa yadda ya kamata.
Ya ce layin waya marar rajista yana da matukar hadari, wanda ya kamata hukumar ta dauka da muhimmanci.
Ya yi wannan kira lokacin da ayarin hukumar ya kai masa ziyara a ofishinsa da ke Abuja, inda ya ce a shirye majalisar take da ta taimaka wa hukumar da kudi wajen ganin ta kyautata aikinta.
Gbajabiamila ya bayyana harkar sadarwa a matsayin wata hanya ta ci gaban al’umma, ya ce “Najeriya za ta ci gaba da kula da sashin don ganin ba a bar ta a baya ba.”
Shugaban ya ce yawan mutane yana karuwa a kullum, don haka masu amfani da layin waya za su karu. Ya bukaci Hukumar NNC ta karo kayayyakin aiki. Kuma majalisar za ta shigo don taimakawa da kudin ayyuka. “Za mu yi aiki tare wajen ganin mun cimma nasara kan aiki cikin sauki. Lokacin da hukumar ta bayyana cewa akwai layuka wajen miliyan tara wanda ba su da rajista a Najeriya, dukkanmu mun san matsalar rashin yi wa layuka rijista. Yana da hadari ga tsaro,” inji shi.