✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gawurtattun ’yan bindiga da aka cafke a Zamfara

Gawurtattun ’yan bindiga da aka kashe da wadanda aka kama a Zamfara.

Gawurtattun ’yan bindiga 21 ne aka cafke, bayan an bindige wasu biyar a cikin wata guda da aka katse layin sadarwa a Jihar Zamfara.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta ce gawurtattun ’yan bindigar  na daga cikin mutum 69 da jami’an tsaro suka cafke a watan Satumba, ciki har da wasu mutum 48 da ke hada baki da miyagun.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, SP Muhammed Shehu, ya ce, “’Gawurtattun ’yan bindiga 21 ne aka tsare a sassan jihar, an kuma hallaka wasu biyar.

“An kuma dakile hare-haren ’yan bnidiga hudu, an kama masu kai musu bayanai da dama, wadanda a halin yanzu ake bincikar su kafin a gurfanarwa a gaban kuliya.

“Sannan an kubutar da mutum sama da 200 da aka yi garkuwa da su, an kuma mika su ga iyalansu,” inji shi.

Sai dai kuma bai bayyana sunen manyan ’yan bindigar da aka kama ko wuraren da aka cafke su ba.

A cewarsa, “Daga lokacin da aka fara aiwatar da matakan tsaron da Gwamna Bello Matawalle ya dauka a wata guda da ya gabata, hukumomin tsaro sun kai hare-hare a kan wasu maboyan ’yan bindiga domin kawar da masu kunnen kashin cikinsu daga doron kasa.

“A cikin wata dayan an samu gagarumar nasara tare da karya lagon miyagun da ke ta kai hare-hare suna sace mutane suna kashe wasu.

“Matakan sun kaste wa ’yan bindiga hanyar samun abinci da man fetur da magunguna da sauran bukatunsu, sannan babu halin biyan kudin fansa saboda an katse hanyar sadarwa tsakaninsu da dangin mutanen da suka sace,” inji Shehu.

A cewarsa, “’Yan sanda sun dakile yawan garkuwa da mutane da fashi da kwacen mota da sauran miyagun laifuka.

“Ayyukan ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun samar da aminci a yankuna da kauyukan da a baya suke zaune cikin zullumin yiwuwar ’yan bindiga za su kawo musu hari.

“Yanzu ’yan bindiga ba sa iya ko motsi; masu ba su bayanai ba sa iya tuntubar su ko zuwa wurinsu, ballantana su samu yadda za su cutar da mutane.”

Kakakin ’yan sandan ya ce dawainiyar kula da mutanen da aka sace ta yi wa masu garkuwar yawa, shi ya sa suke sakin su, saboda yadda aka matsa da fatattakar su.

Ya ce abubuwan da aka kwace daga hannun bata-garin sun hada da bindigogi kirar AK47 da bindigogi kirar gida da albarusai da adduna da guraye da layoyi; Akwai kuma kayan masarufi da miyagun kwayoyi da man fetur, sai kuma babura da tsabar kudi.

SP Shehu ya yi roko ga al’umma da su rika taimaka wa hukumomin tsaro da bayanan da za su taimaka wajen kawar da miyagu daga cikin al’umma, yana mai cewa za a gurfanar da wadanda suka shiga hannun a gaban kotu da zarar an kammala bincike a kansu.