✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gawuna ya kada kuri’a

Ya kada kuri’arsa ce a rumfar zabe mai lamba 41 da ke yankin Gidan Hali na Unguwar Gawuna a Karamar Hukumar Nasarawa.

Dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, ya kada kuri’arsa yayin da zaben gwamna da na ’yan majalisar jiha ke gudana a wannan Asabar din.

Gawuna wanda shi ne Mataimakin Gwamnan Kano, ya kada kuri’arsa ce a rumfar zabe mai lamba 41 da ke yankin Gidan Hali na Unguwar Gawuna a Karamar Hukumar Nasarawa da misalin karfe 9:51 na wannan safiyar.

Yayin isarsa mazabar da misalin karfe 9:44, jama’ar da suka hallara a rumfar zaben sun yi masa yekuwar goyon baya da fatan samun nasara.

Aminiya ta ruwaito cewa, gabanin wannan lokaci, ana zaman dar-dar ne a mazabar inda har ta kai jami’an ’yan sanda sun bukaci karin ma’aikata domin tunkarar duk wani lamari na ko ta kwana.

Ana dai ganin cewa dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ne babban kalubalen da Gawuna zai yi fatan samun galaba a kansa a wannan zaben.

%d bloggers like this: