✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gawarwakin mutanen da aka yi garkuwa da su sun fara rubewa a hannun ’yan bindiga

Dakarun sojin sun yi wa maharan kwanton-bauna.

Dakarun rundunar tsaro ta ‘Operation Thunder Strike/Whirl Punch’ ta ce ta gano yadda gawarwakin wasu mutane da aka yi garkuwa da su sannan aka kashe su suka fara rubewa a hannun ’yan bindiga a Jihar Kaduna.

Daraktan yada labarai na Hedkwatar Tsaro ta Kasa, Manjo-Janar Benard Onyeuko ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja, ranar Alhamis.

Kakakin ya kuma ce dakarun sun kashe ’yan bindiga 55 a yankin Labi da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Ya ce dakarun sun fatattaki ’yan bindigar a wasu hare-hare daban-daban da suka kaddamar musu.

Kakakin rundunar, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya ce dakarun sun gano gawarwakin mutane da dama da aka yi garkuwa da su a maboyar ’yan bindigar.

Ya ce tuni gawarwakin sun fara rubewa a lokacin da sojojin suka kai farmakin a ranar Laraba.

Kazalika, kakakin ya ce wasu dakarun soji a ranar Laraba sun kai farmaki kan wasu sansanin ’yan awaren Biyafara da ke yankunan Ihiala da Orsulu na Jihohin Anambra da Jihar Imo.

“A yayin aikin share fage, sojojin sun gano gawarwakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma wasu da ake zargin ’yan awaren ne suka kashe su sannan suka jefa gawarwakin a cikin wata rijiya mai zurfi,” inji Kakakin.