✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gaskiyar wasikar harin ’yan bindga a FGC Sakkwato

An baza jita-jita cewa ’yan bindiga sun tura wasika cewa za su kai hari makarantar.

Labarun karya sun yi ta yawo cewa ’yan bindiga sun aike wa Kwalejin Gwamantin Tarayya (FGC) da ke Sakkwato wasikar cewa za su kai mata hari.

Rufe makarantar kwanar da aka yi kafin lokacin da ya kamata ya haifar da zargin cewa hukumar makarantar ta yi hakan ne saboda barazanar da ’yan bindiga suka yi mata.

Aminiya ta gano cewa mutane da dama (ba dalibai ko ma’aikatan makarantar ba) sun yi ta tura wa iyayen daliban FGC Sakkwato sakonni cewa su je su kwashe ’ya’yansu, ’yan bindiga sun aiko wasika cewa za su kai hari makarantar.

Hakan ya faru ne bayan wasu daliban makarantar sun yi yunkurin komawa gidajensu, bisa zargin cewa an aike wa hukumar makarantar takardar da ake rade-radi.

Amma hukumar makarantar ta FGC Sakkwato ta musanta rufe makarantar saboda wata barazana ko ma samun wata wasika daga ’yan bindgiar kamar yadda ake rade-radi.

Shugaban Makarantar, Ibrahim Uba, a cikin wata sanarwa, ya ce, “Muna so a sani cewa a ranar Litinin 13 ga Satumba, 2021 wasu daliban FGC Birnin Yauri da aka dawo da su wurinmu bayan harin da aka kai makarantu sun taru cewa za su koma gida saboda wata wasika da ake riya cewa ’yan bindiga sun aiko mana (hukumar makarantar), wanda hakan ya jefa dalibai da malamai cikin zullumi.

“Amman hukumar makarantar ta samu ta shawo kansu ta kuma bayyana musu cewa ita dai babu wata wasikar da ’yan bindiga ko wasu masu laifi suka aiko mata, ballanta wata barazanar tsaro,” inji sanarwar.

Ya kara da cewa daga baya ne hukumar makarantar ta ga dacewar rufe makarantar.

“Bayan ta tattauna da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, sai hukumar makarantar ta yanke shawarar rufe makarantar domin kawar da duk wata fargaba, musamman kuma lura da cewa dalibai sun riga sun kammala jarabawarsu da canjin aji.”

Amma ya jaddada cewa labarin da ke ta yawo a kafafen sadar da zumunta kanzon kurege ne, kuma a kodayaushe FGC Sakkwato da hukumomin tsaro suna tuntubar juna domin tabbatar da tsaro da aminci dalibai da malamai da sauran ma’aikata.

“Duk da cewa an yi gaggawar rufe makarantar, an yi kyakkyawan tsari da sauran daliban da suka rage da suke rubuta jarrabawar WAEC”, injin shugaban makarantar.