✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gasar Zakarun Turai: Wasannin da za a fafata a ranar Talata

Za a ci gaba da wasa na hudu-hudu a cikin rukuni a gasar Zakarun Turai wato Champions League ranar Talata, inda za a yi karawa…

Za a ci gaba da wasa na hudu-hudu a cikin rukuni a gasar Zakarun Turai wato Champions League ranar Talata, inda za a yi karawa takwas.

Z­a a buga wasannin ne da misalin karfe  karfe 8:00 na dare. Sai dai tuni aka yi nisa a wasan Manchester City da FC Copenhagen wanda aka fara tun da misalin karfe 5:45 na Yammacin Talatar nan.

Ga rukunai da kungiyoyin da za su fafata a daren:

Rukuni na 5

Ac Milan vs Chelsea

Dinamo Zagreb vs Red Bull Salzburg

Rukuni na 6

Celtic da RB Leipzig

Shakhtar Donetsk da Real Madrid

Rukuni na 7

FC Copenhagen da Manchester City

Borussia Dortmund da Sevilla

Rukuni na 8

Paris Saint-Germain da Benfica

Maccabi Haifa da Juventus

Ana dai ganin cewa, wasan da zai fi zafi a rukuni na biyar shi ne fafatawar da za a yi tsakanin AC Milan da Chelsea.

A rukuni na shida kuwa, wasan da zai fi daukar hankali shi ne wanda za a gwabza tsakanin Real Madrid mai rike da kofin da Shahktar Donetsk da.

Wasan da za a kai ruwa rana tsakanin Sevilla da Borussia Dortmund shi ne zai fi daukar hankali a rukuni na bakwai.

%d bloggers like this: