✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gasar Zakarun Turai: Fashin baki kan wasannin ranar Talata

Aminiya ta kalato muku irin wainar da aka toya wasannin.

A ranar Talata ce aka buga wasanni na hudu na cikin rukuni a gasar Zakarun Turai wato Champions League.

Aminiya ta kalato muku irin wainar da aka toya wasannin:

Rukuni na 5

Dinamo Zagreb 1-1 Salzburg

Milan 0-2 Chelsea

Kamar yadda aka tashi wasannin rukuni na 5, a karawar da kungiyar Chelsea ta yi da AC Milan, ta samu nasara a kanta sau biyu a jere.

Hakan shi ne ya ba Chelsea damar jagorantar rukunin da maki 7, sai kuma  Salzburg da take mataki na biyu da maki 6.

AC Milan wadda ta hada maki hudu ita ce ta 3 yayin da ita ma Dinamo Zagreb mai maki 4 a wasannin da ta buga, sai dai ta kasancewa a karshen rukunin saboda bambancin zura kwallo a raga da ke tsakaninta da AC Milan.

Kungiyar Chelsea da Salzburg za su samu gurbi a zagaye ‘yan 16 muddin suka ci wasansu na gaba.

A bangare daya kuwa, akwai yiwuwar AC Milan da Dinamo Zagreb ba za su kai labari ba a gasar Cin Kofin Zakarun Turai duba da an ba su tazarar maki.

Rukuni na 6

Celtic 0-2 RB Leipzig

Shakhtar 1-1 Real Madrid

A rukuni na 6 kuwa, Real Madrid ce ke jagorantarsa bayan ta hada maki 10 a cikin wasanni hudu da ta buga.

RB Leipzig ce ke biye mata a mataki na biyu da maki 6, yayin da Shakhtar ta kasance ta uku da maki 5.

Celtic kuwa tana da maki 1 tal, lamarin da ya sa ta ke ta karshe a rukunin.

A wannan rukuni kuwa za a iya cewa har yanzu tana kasa tana dabo a tsakanin kungiyar RB Leipzig da ke da maki 6 da Shakhtar mai maki 5, wanda kowannen su zai iya kai labari duba da babu wani tazarar maki sosai a tsakaninsu.

A bangaren Celtic kuwa, zai yi wahala ta iya fitowa daga gurbin duba da fintinkau da aka yi mata.

Rukuni na 7

Dortmund 1-1 Sevilla

Copenhagen 0-0 Man City

A rukuni na 7 kuwam Man City ita ce ke jagoranci da maki 10, sai Dortmund da take bin ta da maki 7, kungiya ta uku kuwa ita ce Sevilla da maki 2, sai Copenhagen da ta zo a ta hudu da maki 2.

Da yake a wannan rukunin alamu sun nuna Man City ta riga da samu kai wa zagayen ‘yan 16 na gasar, hakazalika ita ma Dortmund idan har ta ci wasanta na gaba, za ta samu kai wa zagayen na gaba.

Har ila yau, alamu sun nuna Sevilla da takwararta Copenhagen ba za su kai labari ba saboda nisan da aka yi musu na maki a rukunin.

Rukuni na 8

PSG 1-1 Benfica

Haifa 2-0 Juventus

Kungiyar PSG ita ce ta daya a rukuni na 8 da maki 8, sai Benfica ita ma da take binta a matsayi na biyu da maki 8.

Kungiya ta uku kuwa a rukunin ita ce Juventus da ke da maki 3 sai Maccabi Haifa a ta hudu da maki 3.

Wannan rukuni, rukuni ne mai dan sarkakiya saboda na daya da na biyu dukansu maki daya suke da shi wato PSG da Benfica, idan har wadannan kungiyoyin suka ci wasanninsu na gaba to su ma za su samu zuwa zagaye na gaba.

Sai dai kuma kungiyar Juventus da Maccabi Haifa sun saddakar cewa ba za su kai labari ba muddin wadancan kungiyoyin biyu suka ci wasanninsu.