✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Zakarun Kuloba Na Turai: Yau za a yi jadawalin Semi-Fainal

A yau Juma’a 13 ga watan Afrilu ne ake sa ran za a gudanar da Jadawalin Gasar Zakarun Kulob na Turai (Champions League) matakin kusa…

A yau Juma’a 13 ga watan Afrilu ne ake sa ran za a gudanar da Jadawalin Gasar Zakarun Kulob na Turai (Champions League) matakin kusa da na karshe (Semi Fainal).

Jadawalin zai gudana ne a hedkwatar Hukumar shirya kwallo a Nahiyar Turai (UEFA) da ke Nyom na kasar Suwizilan da misalin karfe 12 na rana agogon Najeriya.

Sannan hukumar za ta yi jadawalin ne na gasanni biyu a lokaci guda, wato na zakarun kulob na Turai da kuma na Gasar Europa.

Za a yi jadawalin ne a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa hudu da suka kai wannan mataki.  kungiyoyin su ne kulob din FC Roma na Italiya da Liberpool na Ingila da kulob din Real Madrid na Sifen da kuma Bayern Munich daga Jamus.

Kamar yadda tsarin ya nuna, kowace kungiya za ta iya haduwa da ’yar uwarta ko da sun fito daga kasa daya ne. Sai dai kawo yanzu babu wani kulob biyu da suka fito daga kasa daya da suke kai wannan mataki.  Dukkan kulob hudun sun fito ne daga kasashe daban-daban.

Bayan an kammala jadawalin, za a fara wasannin farko ne a ranar 24 da kuma 25 ga wannan wata na Afrilu yayin da za a yi wasa zagaye na biyu a ranakun 1 da kuma 2 ga watan Mayu, 2018.  

A ranar 26 ga watan Mayu, 2018 ne za a yi wasan karshe a filin wasa na Olimpiyskyi da ke birnin Kyib na Rasha daga nan ne za a tantance kulob din da zai dauki kofin.

Idan ba a manta ba kulob din Real Madrid ne ya lashe kofin sau biyu a jere, sannan a bana ma yana yunkurin lashe kofin a karo na uku.  Sai dai kungiyoyin da suka kai wannan mataki irin su Liberpool da Bayern Munich da Roma suna yunkurin ganin sun samu nasarar lashe wannan kofi a wannan karo.

Masoya kwallon kafa sun zuba ido su ga yadda jadawalin da wasannin za su kaya.  Hausawa dai na fadin ‘ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare’.