A jibi Lahadi idan Allah Ya kaimu, kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles za ta kece-raini da kasar Habasha (Etofiya) a gasar neman gurbin zuwa cin kofin duniya da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa.
Za a gudanar da wasan ne a filin wasa na garin Etopiya yayin da za a yi wasa zagaye na biyu a Najeriya a watan gobe.
Duk kasar da ta samu nasara a wasannin biyu za ta haye zuwa gasar cin kofin duniya da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa.
Najeriya dai ita ce ta 36 a jerin kasashen da suka fi kwazo a duniya a jadawalin da Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar a watan jiya yayin da Habasha ta kasance ta 93.
Sai dai a harkar kwallo ba a nan gizo ke sakar ba idan aka yi la’akari da yadda Etopiya ta yi wa kasar Afirka ta Kudu kancal a rukunin da suka fafata na neman hayewa zuwa wannan mataki. Etopiya ce ta samu nasara a wasan da ta yi da Afirka ta Kudu da hakan ta sa ta kasnace ta daya a rukunin da suka fafata kuma ta hauro zuwa wannan mataki. Tuni Afirka ta Kudu ta yi waje a neman hayewa gasar cin kofin duniya don haka abu ne mai sauki Etopiya ta ba Najeriya mamaki a wannan lokaci idan ta nemi rainata.
Habasha ta sha alwashin yi wa Najeriya cikas a wannan karo musamman a kokarinta na neman hayewa gasar cin kofin duniya a karon farko a tarihin gasar.
Sai dai kungiyar Super Eagles ta nuna da gaske take don ta shirya wa wasan sosai. Tuni zaratan ’yan kwallon Najeriya da ke buga wasa a sassan duniya suka halarci sansanin horar da su don samun horon da ya kamata.
Koci Stephen Keshi ya nuna ba za su yi sakwa-sakwa wajen raina ’yan kwallon Etopiya a wannan lokaci ba, don ya san hatsarin da ke tattare da hakan.
“Harkar wasa ba babba, ba yaro a wannan lokaci”, inji Keshi a lokacin da yake hira da ’yan jaridu kafin su bar kasar zuwa Habasha.
…Jonathan zai yi wa Super Eagles goma ta arziki idan suka haye gasar cin kofin duniya
Shugaban kasa Goodluck Jnathan ya nanata aniyarsa ta yi wa kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles goma ta arziki idan suka samu damar hayewa gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa.
Bayanin haka yana kunshe ne a lokacin da Darakta-Jananar na Hukumar da ke kula da sha’anin wasanni na kasa (National Sports Commission) Gbenga Elebeleye yake hira da kafar sadarwar MTNFootball.com.
Ya ce an shirya yi wa kungiyar Super Eagles goma ta arziki muddin suka haye gasar cin kofin duniya.
“Mun fara shirya yi wa daukacin kungiyar abin alheri idan suka fitar da kasar nan kunya na hayewa zuwa gasar cin kofin duniya kuma tuni shugaban kasa Jonathan ya bayar da umarni a fara shirin yin haka don mun tabbatar kungiuyar za ta samu nasara a wasanni biyu da za ta kara da Etopiya”, inji Gbenga.
Idan ba a manta ba a watan Fabrairun wannan shekara da muke ciki ne Shugaba Goodluck Jonathan ya yi wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ruwan Naira baya ga kyaututtukan da suka hada da gidaje da kuma filaye da ya yi musu jim kadan da lashe kofin Afirka a karo na uku a kasar Afirka ta Kudu.
Masana harkar kwallo suna ganin a wannan karo ma shugaban zai cika alkwarin da ya yi musu muddin suka ba marada kunya na samun nasara a wasannin da za su kara da Etopiya da hakan zai ba Najeriya damar halartar gasar cin kofin duniya a Brazil a badi idan Allah Ya kaimu.