A gobe Asabar 14 ga wannan wata da muke ciki ne ake sa ran za a yi wasan karshe a gasar rukuni-rukuni na Sifen da aka fi sani da La-Liga.
kungiyoyin kwallon kafa biyu ne suke sahun gaba a teburin gasar wadanda ake sa ran daya daga ciki ne zai zama zakara a gasar ta bana.
kungiyar kwallon kafa ta FC Barcelona ce take saman tebur da maki 88 yayin da kulob din Real Madrid yake biye da maki 87.
FC Barcelona za ta yi wasanta na karshe ne da kulob din Granada a waje yayin da Real Madrid za ta yi wasanta na karshe ne da kulob din Deportibo La-Coruna a waje.
Idan FC Barceona ta samu nasara a wasan, ita za ta kare kamubunta, tun da ita ce zakara a kakar wasan da ya wuce. Idan Real Madrid kuma ta samu nasara yayin da FC Barcelona ta samu rashin nasara ko ta yi kunnen doki, ko shakka babu Madrid ce za ta zama zakara a gasar ta bana.
Ana sa ran gidajen kallon kwallo a Najeriya za su cika makil don ganin yadda wasannin za su kaya.
Gasar La-Liga: Gobe za a san kulob din da zai zama zakara
A gobe Asabar 14 ga wannan wata da muke ciki ne ake sa ran za a yi wasan karshe a gasar rukuni-rukuni na Sifen da…