✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar La-Liga:  Gobe Atletico Madrid za ta hadu da FC Barcelona

A ci gaba da fafatawa a gasar rukunin La-Liga na Sifen, a gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a kece raini a tsakanin kulob…

A ci gaba da fafatawa a gasar rukunin La-Liga na Sifen, a gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a kece raini a tsakanin kulob din Atletico Madrid da kuma na FC Barcelona da ke Sifen.

Wasan zai gudana ne da misalin karfe 7:45 na dare agogon Najeriya a filin wasan Atletico.

Kawo yanzu FC Barcelona ce take saman teburin gasar da maki 24 sai Sevilla ta biyu da maki 23 sai Atletico ta uku da maki 23 sai Alaves ta hudu da maki 23.

Kenan idan Atletico Madrid ta samu nasara a kan FC Barcelona za ta iya hayewa teburin gasar, amma idan FC Barcelona ce ta samu nasara za ta ci gaba da zama ta daya a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar.

Ana sa ran gidajen kallon kwallon kafa za su cika makil da masoya kallon kwallo don ganin yadda wasan zai kaya.

Idan za a tuna a wancan mako ne kulob din Real Betis ya lallasa FC Barcelona da ci 4-3 da hakan bai yi wa magoya bayan kungiyar dadi ba.