✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar La-Liga: An canza ranar wasan Madrid da Barcelona

A ranar Litinin da ta wuce ne Shugaban Hukumar Shirya kwallon kafa ta Sifen (FA) Jabier Tebas ya bayyana cewa hukumarsa ta canza ranar da…

A ranar Litinin da ta wuce ne Shugaban Hukumar Shirya kwallon kafa ta Sifen (FA) Jabier Tebas ya bayyana cewa hukumarsa ta canza ranar da za a yi wasa a tsakanin kulob din Real Madrid da FC Barcelona a gasar rukunin La-Liga na Sifen.  Shugaban ya ce yanzu wasan zai gudana ne a ranar Asabar 23 maimakon Laraba 20 ga watan Disambar 2017 da misalin karfe 1 na rana agogon Najeriya.

Tun farko an shirya wasan zai gudana ne a ranar Laraba 20 ga watan Disambar 2017 amma saboda kulob din Real Madrid zai halarci Gasar Club World Cup da zai gudana a ranar 17 ga watan Disambar 2017 ne ta sa hukumar ta canza ranar  zuwa 23 ga watan Disamba don a ba Madrid damar samun isasshen hutu kafin wasan.

Wasa a tsakanin kulob din Real Madrid da na FC Barcelona da ake masa lakabi da El-Clasico shi ne mafi zafi a Sifen don an kiyasta kimanin mutane miliyan 500 ne a sassan duniya suke kallon wasan walau a filin wasan da kuma a akwatunan talabijin dinsu.