Sarkin Qatar Sheikh Tamin bin Hamad Al Thani ya koka da irin suka da kasar ke sha daga ‘yan gaza gani kan batun gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a kasar.
A cewar Al Jazeera, tun lokacin da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta ayyana kasar a matsayin wacce za ta karbi bakuncin gasar a 2010, Qatar take narka biliyoyin daloli a shirye-shiryen daukar nauyin gasar.
- Qatar 2023: Muhimman abubuwa kan karamar kasa mai tarin arziki
- An fara zagayen karshe na sayar da tikitin kallon cin kofin duniya a Qatar
Tun daga lokacin kuma kasar take ta fuskantar suka da tuhume-tuhume daban-daban, kama daga bakin ma’aikata da za ta dauka, zuwa kare hakkin mata har masu goyon bayan ‘yan luwadi da madigo.
“Tun da muka yi nasarar samun wannan damar ta daukar nauyin wannan gasar, aka yi wa Qatar rubdugu da sukar da babu kasar da aka taba yi wa haka,” in ji sarkin a jawabinsa ga Majalisar Kasar.
Shi kuwa Shugaban FIFA, Gianni Infantino cewa yake, wannan gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a Gabas ta Tsakiya, za ta kasance wadda ta fi duk wadanda aka taba yi a shekarun baya.
Za a soma gasar Cin Kofin Duniya ce a ranar 20 ga watan Nuwambar 2022.