Gwammatin Qatar na shirin rage yawan ma’aikata da za su rika zuwa aiki da kuma sa’o’in karatu a makarantu kafin da kuma a lokacin Gasar Cin Kofin Duniya da kasar za ta karbi bakunci.
A ranar Laraba Wani jami’in gwamnatin Qatar ya ce majalisar gudanarwar kasar ta rage sa’o’in aiki zuwa hudu, tare da rage yawan ma’aikatan da za su rika zuwa aiki a zuwa kashi daya bisa biyar daga ranar 1 ga watan Nuwamba zuwa ranar 19 ga Disamba, 2022.
- Ana zargin maganin tari ya kashe yara 66 a Gambiya —WHO
- Ranar Malamai: Daliban Kano na neman a inganta walwalar malamai
Daga ranar 1 zuwa 17 ga watan Nuwamba kuma lokacin halartar makarantu zai koma daga karfe 7 na safe zuwa 12 na rana, sannan a bai wa dalibai hutu daga 18 ga watan zuwa 22 ga watan Disamba.
Za kuma a hana motoci bin Babban Titin Corniche da ke makwabtaka da teku a Doha, babban birnin kasar, daga ranar 1 ga watan Nuwamba.
A halin yanzu dai ana gina masaukan magoya bayan tawagar ’yan wasan kasashe a kusa da babbar hanyar da ke birnin Doha.
Akalla mutum miliyan daya ne ake sa ran za su je kallon Gasar Cin Kofin Duniya da za a fara daga ranar 20 ga watan Nuwamba, zuwa 18 ga Disamba, 2022.
Ganin haka ne gwamnatin Qatar ta fara daukar matakan rage cunkoson ababen hawa a kan tituna masu makwabtaka da filayen wasa takwas da za a buga wasannin gasar.
Hukumomin kasar sun fi mayar da hankali a kan makonni biyu na farkon gasar, wanda a lokacin ne ’yan kallo za su fi yawa domin halartar wasannin da tawagar ’yan wasan kasashe 32 za su fafata.