✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gasar Kofin Duniya: Jamus ta sha kashi a hannun Japan

Jamus ta yi rashin nasara a wasan farko na Gasar Kofin Duniya.

Jamus ta fara wasanta na farko a Gasar Kofin Duniya da kafar hagu, inda ta yi rashin nasara da ci 2 da 1 a fafatawar da ta yi da tawagar Japan a ranar Laraba.

Wasan shi na farko a rukuni na biyar wanda aka soma da misalin karfe 2 na yamma agogon Najeriya.

Dan wasan tsakiyar Jamus, Ilkay Gundogan ne ya fara zura kwallo a bugun fenareti a minti na 33 da fara wasan.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne tawagar Japan ta zare kwallon ta hannun dan wasan tsakiyarta, R. Doan a minti na 75.

A minti na 83 ne Japan din ta sake jefa kwallo ta biyu ta hannun dan wasanta Asano.

Jamus dai ta kai hare-hare har guda 27, amma guda takwas ne kacal suka zama masu hatsari.

Ita kuwa Japan ta kai hare-hare guda 11, wanda daga ciki uku ne kacal masu hatsari a wasan.