Jamus ta fara wasanta na farko a Gasar Kofin Duniya da kafar hagu, inda ta yi rashin nasara da ci 2 da 1 a fafatawar da ta yi da tawagar Japan a ranar Laraba.
Wasan shi na farko a rukuni na biyar wanda aka soma da misalin karfe 2 na yamma agogon Najeriya.
- Dalilin da na amince a sauya fasalin takardun kudi —Buhari
- Turji ya tsare ’yan aike bayan sun kai masa harajin N10m
Dan wasan tsakiyar Jamus, Ilkay Gundogan ne ya fara zura kwallo a bugun fenareti a minti na 33 da fara wasan.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne tawagar Japan ta zare kwallon ta hannun dan wasan tsakiyarta, R. Doan a minti na 75.
A minti na 83 ne Japan din ta sake jefa kwallo ta biyu ta hannun dan wasanta Asano.
Jamus dai ta kai hare-hare har guda 27, amma guda takwas ne kacal suka zama masu hatsari.
Ita kuwa Japan ta kai hare-hare guda 11, wanda daga ciki uku ne kacal masu hatsari a wasan.