✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Firimiyar Ingila: Gobe za a shawo ta tsakanin Arsenal da Man United

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a yi wasa mai zafi a gasar rukunin firimiyar Ingila a tsakanin manyan kulob biyu wato Arsenal…

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a yi wasa mai zafi a gasar rukunin firimiyar Ingila a tsakanin manyan kulob biyu wato Arsenal da kuma Manchester United.    Wasan zai gudana ne da misalin karfe 6:30 na yamma agogon Najeriya a filin wasan Arsenal da ake kira Emirate Stadium.

Wannan wasa, yana daga cikin wadanda suka fi zafi a gasar ta firimiya don a duk lokacin da kungiyoyin biyu suka hadu dubban magoya baya ne ke yin tururuwa don ganin yadda wasan ke gudana.

Kawo yanzu kulob din Manchester United ne yake matsayi na biyu a teburin gasar yayin da Arsenal ke matsayi na hudu bayan an yi wasanni 14.

Sai dai kamar yadda jadawalin gasar ta nuna, duk kulob din da ya samu rashin nasara a wasan, to takwarorinsa za su iya yi masa nisa, musamman ganin yadda gasar ta fara daukar zafi.

Tuni kocin Arsenal Arsene Wenger da kocin United Jose Mourinho suka shirya tunkarar wasan.  Ana sa ran gidajen kallon kwallo za su cika makil don ganin yadda wasan zai kaya.