✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar firimiya ta Ingila: Jibi za a kece raini a tsakanin City da United

A jibi Lahadi idan Allah Ya kaimu za a kece raini a tsakanin kulob din Manchester City da kuma na Manchester United da ke Ingila…

A jibi Lahadi idan Allah Ya kaimu za a kece raini a tsakanin kulob din Manchester City da kuma na Manchester United da ke Ingila a gasar rukunin firimiya n. &nbsp
Wasan zai gudana ne da misalin karfe biyar agogon Najeriya sannan zai yi zafi ganin cewa za a hadu ne a tsakanin kungiyar da take matsayi na 4 da kuma ta 5 a teburin gasar.
Manchester City ce take matsayi na hudu bayan ta hada maki 51 yayin da United kuma take matsayi na biyar da maki 47.
Kulob din Leicester City ne yake saman teburin gasar da maki 63 sai na Tottenham da ke biye da maki 58 sai kuma na Arsenal a matsayin ta uku da maki 52 sai Man City a matsayi na hudu da maki 51.
Kulob din Leicester da na Tottenham suna haskakawa a bana ganin cewa kawo yanzu su ke jan ragamar gasar kuma akwai yiwuwar daya daga cikinsu ne zai kafa sabon tarihi a gasar wajen daga kofin firimiya na bana.