Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sadik Sani Bello ya umurci Kwamishinan kula da Harkokin Kudi na Jihar ya gaggauta samar wa kungiyar kwallon kafa ta Neja Tornadoes Naira miliyan 25 don tunkarar gasar firimiya ta bana da za a fara a jibi Lahadi idan Allah Ya kaimu.
Alhaji Abubakar Sadik Sani Bello ya bayar da umurnin ne bayan da Shugaban Hukumar Gudanar da kungiyar kwallon kafar ta Neja Tornadoes Malam Adamu Aliyu Muhammad ya gabatar da wasu daga cikin muhimman kalubalen da suka zame wa kungiyar karfen kafa ana gab da fara gasar wasannin bana da suka hada da Naira miliyan 25 kudin ka’ida da kuma motar da kungiyar za ta yi amfani da ita wurin gudanar da harkokinta yadda ya kamata.
Gwamnan wanda ya bayyana farin cikinsa ganin yadda kungiyar ta yi namijin kokari a wasannin da ta gudanar a bara wadanda suka taimaka mata ta samu nasarar lashe gasar rukuninsu, sannan kuma ta lashe na zakaru na kasa da aka gudanar wato ‘Super Four’ da akan gudanar duk shekara duk da dimbin matsalolin da suka addabi kungiyar, don haka ya zama wajibi a samar mata duk wani abinda ya kamata da zai kai ta ga samun nasara a gasar ta bana.
Ya cigaba da cewa,’a gaskiya ina alfahari da wannan kungiyar don kuwa ba mallakar wani ko wasu ba ne, kungiya ce ta al’ummar Jihar Neja wadda kowa ke bugun kirji da ita,don kuwa ita kadai muke da ita a matsayin da ta samu kanta.Ba za mu yarda ta sake fada wa cikin wani hali da zai hanata samun nasara ba a gasar bana don tana iya lashe wa.A gwamnatancce duk wani abinda kuke bukata za mu samar muku.Ina mai tabbatar muku samun sabuwar mota kafin ku fara wasan farko a gasar bana,don wadda kuke amfani da ita a halin yanzu ta gaji’
Ya yaba wa Hukumar Gudanar da kungiyar ganin irin rawar da ta taka cikin lokaci kankane da aka damka musu wannan gagarumin aikin mai tattare da kalubale.Ya sanar cewa a duniya kowa ya san harkar wasanni na da matukar ribar da duk wanda ya daure ya zuba jari a ciki,cikin lokaci kankane zai ci ribar da za ta taimaka a fannoni daban-sdaban.
Gasar firimiya ta bana: An ba Neja Tornadoes Naira miliyan 25
Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sadik Sani Bello ya umurci Kwamishinan kula da Harkokin Kudi na Jihar ya gaggauta samar wa kungiyar kwallon kafa ta…