A ci gaba da fafatawa a gasar Firimiya ta Ingila mako na 29, a jibi Lahadi ne za a yi gumurzun birnin Manchester a tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa biyu da ke gasar wato Manchester United da Manchester City.
Za a yi wasan ne a filin wasa na Old Trafford wato gidan United da misalin karfe biyar da rabi na yamma agogon Najeriya.
Masoya kwallon kafa za su kashe kwarkwatar ido don ganin yadda wasan zai kaya kamar yadda jadawalin gasar ya nuna.
Kawo yanzu kulob din Manchester City ne na biyu a teburin gasar bayan ya hada maki 57 a wasa 27, yana da kwantan wasa daya yayin da Manchester United ke matsayi na biyar da maki 42 a wasa 28.
Masoya kwallon kafa suna yi wa wannan wasa da kirari da ‘Karon Battar Birnin Manchester, ko kuma “El-Clasico na Ingila” saboda wasan yana daga cikin wasanni mafiya zafi a Ingila.
Tuni kocin United, Ole Gunnar Solksjaer da na City Pep Guardiola suka shirya don tunkarar wannan wasa.
Idan za a tuna Manchester United ce ta doke ta Man. City da ci 2-1 a wasansu na farko.