✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Firimiya: Jibi Liberpool za ta gwabza da Chelsea

A jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu, za a yi wasa mai zafi a gasar rukunin Firimiya ta Ingila a tsakanin kulob din Liberpool da…

A jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu, za a yi wasa mai zafi a gasar rukunin Firimiya ta Ingila a tsakanin kulob din Liberpool da Chelsea.  Za a yi wasan ne a filin wasa na Liberpool da misalin karfe hudu da rabi na yamma agogon Najeriya.

Wasan zai yi zafi ne ganin kungiyar da take saman tebur wato Liberpool ce za ta hadu da ta uku wato Chelsea a gumurzun.

Kawo yanzu Liberpool ce take saman teburi da maki 82 bayan ta yi wasanni 33 sai Manchester City ke biye da maki 80 a wasanni 32 sai Chelsea ta uku mai maki 66 a wasanni 34 sai kuma Tottenham a matsayi ta hudu da maki 63 a wasanni 32.

Yayin da Liberpool take hankoron ganin ta lashe wasan wanda hakan zai iya ba ta damar daga kofin Firimiya a bana, ita kuwa Chelsea tana neman nasara ce don ta kasance daya daga cikin kungiyoyi hudu da za su gama a saman teburin gasar don ta samu damar halartar gasar Zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.

Masana harkar kwallon kafa sun yi hasashen wasan zai yi zafi kuma masoya kwallon kafa za su kashe kwarkwatar ido domin alamu sun nuna wasan zai kayatar.

Haka kuma ana sa ran gidajen kallon kwallon kafa za su cika makil ga masoya kwallon kafa musamman magoya bayan kungiyoyin biyu.

Liberpool dai tana takama da zaratan ’yan kwallo irin su Sadio Mane da Mohammed Salah da Firminho da sauransu, yayin da kulob din Chelsea ke takama da zaratan ’yan kwallo irin su Eden Hazard da Pedro da Willian da sauransu.

Yanzu dai duniya ta zuba ido ta ga yadda wasan na jibi zai kaya.