A ranar Talatar da ta wuce ne Shugaban kasar Kwaddebuwa Alassane Outtara ya yi wa ’yan kwallon kasar ruwan Naira da kuma ba su kyautar gidaje saboda nasarar da suka samu na lashe gasar cin kofin Afirka da aka kammala a ranar Lahadin da ta wuce a Ekuatorial Guinea. kasar ta samu nasarar ce a wasan karshen da ta yi da Ghana a bugun fanafiti da ci 9 da 8.
Shugaban ya yi musu wannan kyauta ce a lokacin bikin karrama su da yi a babban filin wasa na a kasar a ranar Talatar da ta wuce.
Shugaban ya ce ya ba kowane dan kwallon kyautar Yuro dubu 46 da ya yi daidai da Naira miliyan 10 da dubu 764 da kuma gida kimarsa ta kai daidai da kudin da aka ba kowannensu watau Yuro dubu 46.
Haka kuma shugaban ya ba kocinsu dan asalin Faransa mai suna Herbe Renard kyautar Yuro dubu 114 da ya yi daidai da Naira miliyan 26 da dubu 676.
Shugaban ya yaba wa kocin da daukacin ’yan kwallon a kan daukaka martabar kasar na lashe gasar cin kofin Afirka a karo na 30 bayan kasar ta dauki tsawon lokaci ba tare da lashe kofin ba.
Idan za a tuna, rabon da Kwaddebuwa ta lashe gasar cin kofin Afirka tun cikin shekarar 1992 watau kimanin shekara 23 da suka gabata.
Tuni ’yan kwallon da klocin suka nuna farin cikinsu a kan wannan karramawa da shugaban ya yi musu, kuma sun sha alwashin cigaba da nuna kwazo na ganin sun sake lashe kofin a gasar da za ta gudana nan da shekaru biyu masu zuwa.
Gasar Cin Kofin Afirka 2015: Kwaddebuwa ta yi wa ’yan kwallonta ruwan kudi da gidaje
A ranar Talatar da ta wuce ne Shugaban kasar Kwaddebuwa Alassane Outtara ya yi wa ’yan kwallon kasar ruwan Naira da kuma ba su kyautar…
