✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Alkur’ani: An sami gwarzo da gwarzuwa a Jigawa

Gwamnatin Jahar Jigawa ta gabatar da Gasar Musabakar Alkur’ani karo na 23 cikin makon jiya, inda dalibai sama da 200 suka fafata a fagen gasar…

Gwamnatin Jahar Jigawa ta gabatar da Gasar Musabakar Alkur’ani karo na 23 cikin makon jiya, inda dalibai sama da 200 suka fafata a fagen gasar a matakai daban-daban da suka hada da Izifi 10 zuwa Izifi 60 da tafsiri.

A yayin gudanar da musabakar, Maryam Hassan Muhamud daga Karamar Hukumar Kazaure ita ce ta sami maki mafi girma, wato 99.7 tare da tafsiri, inda ta zama gwarzuwar shekara ta bana.

Suleiman Muhammad Usman ne ya amshe kambin gwarzon shekara na gasar ta bana a matakin izifi 60 da tafsiri daga Karamar Hukumar Jahun, inda ya sami maki 83.5.

An yi masa rawani da kandiri da alkyabba da sauran kyaututtuka masu kayatarwa lamarin da ya sa dubban mutane daga Jahun da Kazaure suka cika farfajiyar taron musabakar da aka yi a filin taro na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jahar Jigawa.

A bangaran mata kuma, Maryam Hassan Muhmud ta sami kyaututtuka masu yawa ciki har da babban firji na ruwan sanyi, da keken dinki da kuma na’ura mai kwakwalwa.

Da yake jawabi a wajan taron, shahararren malamin addinin nan Malam Abubakar Gero Arugungun ya ja hankalin al’umma bisa falalar haddar Alkur’ani, yana mai cewa ba yara kadai ya kamata su dukufa ba har manya, ya zama wajibi ga kowa ya haddace Alkur’ani inda hali, ko kuma ya haddace wani sashe.

Haka kuma malamin ya yi amfani da wannan dama, inda ya shawarci jama’a da su zabi mutane nagari a babban zaben da ke tafe, sannan ya yi gargadi bisa zabar mutanen banza wadanda ba su san darajar al’umma da muhimmancin amana ba.

Ya kara da cewa duk Najeriya babu inda gwamnati ta dora mulki daga inda wadda ta dakata sai a Jahar Jigawa, inda ya ce Gwamna Badaru bai yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da ayyukan da ya gada, sai da ya kammala sub a tare da nuna bambancin siyasa ba a cewarsa.

A cikin jawabinsa, Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi ya ce Gwamnatin Badaru ba ta yin wasa da duk wata harka da ta shafi addini, musamman Musabakar Alkur’ani.

Yana mai cewa daga hawan gwamnan zuwa yau, duk abin da suka rubuta suka nema a wajan gwamnati a fagen gasar musabakar bai taba rage wa ba, yadda suka nema haka yake ba su, don haka ya ce ba su da wani abin cewa tsakaninsu da Gwamnatin Badaru a kullum sai dai godiya da sam-barka.

Shi ma a nasa jawabin, Gwamna Badaru ya ce ya gode wa Allah da Ya ba shi ikon bada tallafi a wannan musabaka da sauran sheakarun da suka gabata. Sannan ya yi tsikaci game da shirya musabaka kan sauran fannonin ilimi na Addinin Musulunci, inda ya ce shi ya bada shawarar a fara Jahar Jigawa, amma a halin yanzu ta zama masabaka ta kasa wadda kuma yana alfaharin shi ne sila.

Badaru ya nemi masu shirya gasar na kasa da su kawo gasar da za ayi shekara mai zuwa a Jigawa, kuma ya ce zai dauki nauyin duk dawainiyarsu tun daga farko har zuwa kammala gasar da izinin Allah.

Ya kuma hori wadanda suka amfana da ilimin da su ci gaba da neman ilimi a matsayinsu na dalibai, kasancewar nan gaba su ne jagororin al’umma.