Sakamakon fadi da girman kasar Saudiyya, ana samun tazara mai yawa a lokacin buda-baki a tsakanin yankunan kasar.
Yanki na farko a kasar Saudiyya da yake fara buda-baki a watan Ramadan, shi ne yankin Umm Alzamool, kamar yadda Dokta Abdullah Al-Misnad, wanda
shi ne ya kafa kuma yake shugabantar kwamitin tantance lamuran yanayi, ya bayyana a ranar Litinin da ta gabata a
shafinsa na Twitter.
- An kama mabaraciya da Naira miliyan 13 a Makkah
- Abin da ya sa yaki da ’yan bindiga yake da wahala – Gwamnati
Al-Misnad ya ce masu azumi a yankin Umm Alzamool da ke Kudu maso Gabas a kan iyakar Saudiyya da Oman, su ne suke fara buda-baki da misalin karfe 5:34 na yamma.
Wannan yanki na karkashin Gwamnatin Lardin Al-Ahsa ta Gabas.
Al-Misnad ya ce mutanen karshe da suke yin buda-baki suna yankin Ras Alsheikh Hamid da ke Arewa maso Yammacin Saudiyya, inda suke yin buda-baki da misalin karfe 7.01 na yamma.
Su kuma suna zaune ne a kusa da Akaba a gefen Tekun Maliya a yankin Tabuka.
Tsakanin Umm Alzamool da Ras Alsheikh Hamid akwai nisan kilomita 2,200 da bambancin lokaci da ya kai awa 1:27, kamar yadda Al-Misnad ya tabbatar.
Ya ce lokacin da mutanen Ummu Alzamool suke Sallar Isha’i, a wannan lokaci ne mutanen Ras Alsheikh Hamid
za su yi Sallar Magariba.