✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Garkuwa: ’Yar uwar Ministar Buhari ta kubuta bayan biyan kudin fansa

Dapit Karen, ’yar uwar Ministar Harkokin Mata Pauline Tallen, wacce aka sace a ranar Litinin ta kubuta daga hannun masu garkuwa da ita. Wata majiya…

Dapit Karen, ’yar uwar Ministar Harkokin Mata Pauline Tallen, wacce aka sace a ranar Litinin ta kubuta daga hannun masu garkuwa da ita.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa sai da aka biya kudin fansa na naira miliyan 2.5 sannan Dapit wacce ta shafe kwanaki biyu a hannun masu garkuwar ta kubuta.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Filato, Ubah Gabriel ya bayar da tabbaci kan faruwar lamarin, sai dai ya ki cewa komai game da batun biyan kudin fansa.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Litinin da ta gabata ne wasu ’yan bindiga suka yi awon gaba da Dapit a gidansu da ke unguwar Rantiya a Karamar Hukumar Jos ta Kudu.

Wani dan uwan wacce lamarin ya ritsa da ita wanda ya bai wa wakilinmu tabbaci, ya ce ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 5 na safiya yayin da mazauna yankin ke sharar bacci.

Ya ce da zuwan maharan kai tsaye suka zarce gidansu Dapit, inda suka yi awon gaba da ita kuma daga bisani suka tuntunbi ’yan uwanta a kan biyan fansar Naira miliyan biyar.

%d bloggers like this: