✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garkuwa da mutane na kawo cikas ga manoman zamani

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano cewa manyan manoma na gujewa gonakinsu saboda tsoron masu garkuwa da mutane inda hakan yake yin babbar…

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano cewa manyan manoma na gujewa gonakinsu saboda tsoron masu garkuwa da mutane inda hakan yake yin babbar barazana ga kasuwancin harkokin noma a Najeriya.
Bincike ya gano cewa akwai manyan manoma a sassan kasar daban-daban da suke noma daruruwan hektocin gonaki tare da yin kiwon dabbobi iri-iri.
To amma karuwar satar mutane da ake samu a sassan kasar musamman a yankin Arewaci a yanzu yana barazana ga horkokin noma yayin da manyan manoman su ake hari a sace don neman makudan kudin fansa.
Babban Jami’i a wata gonar zamani da ke kan hanyar garin Jere zuwa Kagarko da ke kan titin Kaduna ya ce masu gonakin zamanin su ake hari inda hakan ya tilasta musu gujewa gonakin nasu.