✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garkuwa da dalibai: Majalisa neman a sa dokar ta-baci kan matsalar tsaro

Majalisar Dattijai ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta sanya dokar ta -baci a kan matsalar tsaro da ke addabar kasar. 

Majalisar Dattijai ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta sanya dokar ta -baci a kan matsalar tsaro da ke addabar Najeriya. 

Majalisar ta bukaci hakan ne bayan kudurin da Sanata Sani Musa daga Jihar Neja ya gabatar yayin zamanta a ranar Laraba.

Sanatan, ya gabatar da kudurin ne bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta garin Kagara a Karamar Hukumar Rafi ta jihar Neja da sanyin safiyar ranar Laraba.

Jihar Neja na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro da garkuwa da mutane inda ’yan bindiga suka addabe ta kamar sauran makwabtanta.

Ko a ranar Talata an samu rahoton halaka mutum 10 da garkuwa da wasu 24 a wani hari da yan bindiga suka kai a wasu yankunan Jihar ta Neja.