Majalisar Dattijai ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta sanya dokar ta -baci a kan matsalar tsaro da ke addabar Najeriya.
Majalisar ta bukaci hakan ne bayan kudurin da Sanata Sani Musa daga Jihar Neja ya gabatar yayin zamanta a ranar Laraba.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da malamai a Neja
- Makarantar Kagara: Gwamnatin Neja ta rufe makarantun kwana
- ’Yan bindiga sun kashe mutane 10, sun yi garkuwa da 24 a Neja
Sanatan, ya gabatar da kudurin ne bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta garin Kagara a Karamar Hukumar Rafi ta jihar Neja da sanyin safiyar ranar Laraba.
Jihar Neja na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro da garkuwa da mutane inda ’yan bindiga suka addabe ta kamar sauran makwabtanta.
Ko a ranar Talata an samu rahoton halaka mutum 10 da garkuwa da wasu 24 a wani hari da ’yan bindiga suka kai a wasu yankunan Jihar ta Neja.