Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, ya ce an ceto ragowar jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC) da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a fadarsa da ke garin Lafia a ranar Talata a lokacin da yake magana game da jami’an da a baya biyu daga cikinsu suka kubuta bayan sun fada tarkon masu garkuwa da mutane a hanyar Mararraba zuwa Udege da ke jihar.
“Ina farin cikin sanar da cewa dukkannin jami’an FRSC da aka sace sun samu ’yanci a ranar Litinin.
“Ina mika godiya ga dukkannin hukumomin tsaro da sauran wadanda suka taimaka wajen kubutar da jami’an”, inji Gwamnan.
Gwamnan ya yaba wa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Bola Longe, da sauran jama’an tsaro da suka ba da gudunmuwa waje ceto ragowar jami’an na FRSC.