Daga hudubar Sheikh Ibrahim Idris
Masallacin Juma’a na Gwallaga, Bauchi
Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya kadaita da girma da daukaka, duk wanda ya yi jayayya da Shi kan wani abu daga cikin su biyun zai damke shi. Na shaida babu abin bauta da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi cikin abin da Ya warware ko Ya kula shi. Kuma na shaida lallai shugabanmu Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa, wanda Ya zabe shi kuma Ya karrama shi. Kuma Ya umarce shi da kaskantar da masu girman kai, kuma Ya kange shi daga sharrinsu. “Ya kai Manzo! Ka isar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka. Idan ba ka aikata haka ba, to, ba ka isar da sakonSa ba. Kuma Allah Yana tsare ka daga mutane. Lallai ne Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai.”
Ya bayin Allah! A wannan zamani namu wasu mutane sun yawaita, da dayansu ke kai kansa fiye da yadda hankali da tunani ke iya dauka. Yana ganin shi mai mukami ne madaukaki, daukaka iya daukakar da ta doke ta kowa. Ba a ambatar wani mai girma a gabansa face ya yi dariya ya girgiza kansa yana mai izgili saboda abin da yake da shi na mukami. Wata maganar hikima na cewa:
“Wanda ya jahilci matsayin kansa, Sai dai wani ya gano masa abin da bai iya gani ga kansa.”
Za ka ga irin wannan mai girman kai yana ji da kansa, yana mai tsananin wauta da ji da kai da nuna isa har ma ga Mahaliccinsa Mai iko, Mai girma, Madaukaki. Za ka gan shi kamar wuta da ke ci bal-bal. Yana mai fusata kan karamar kalmar da ba ta gamsar da shi ba, koda mai fadinta bai nufin komai sai kyautatawa!
Daga cikin alamominsa za ka iske shi mai kwadayin ya kasance a gaban mutane (shugabansu), yana son su rika sauraron maganarsa, amma maganar waninsa tana yi masa zafi koda gaskiya ce. Za ka ga tufafinsa suna jan kasa, a lokacin tafiya zai rika takama yan mai karkata kundukukinsa, koda yana daure da akala za ka iske shi yana mai karkace masa.
Wani kuma za ka ga ya cika gashin bakinsa ya datse gemunsa ya daidaita sajensa kamar kaho. Wani ya rera cewa:
“Lallai kamalar da mutane ke shugabancin da ita, Ita ce natsuwa da hada ilimi da aiki.”
Har wa yau daga cikin alamominsa, za ka iske mai girman kai, ba ya sha’awar fakirai su kusance shi, ba ya rungumar kowa sai masu kudi. Mutakkabiri mai girma kai ba ya so wa muminai abin da yake so ga kansa, domin ba ya iya yin haka ne saboda girman kansa da jiji da kansa. Ba ya iya yin tawali’u alhali shi ne jagoran dabi’un zababbun mutane.
Mutakabbiri ba ya iya barin hasada da kullata kuma ba ya iya dauwama a kan gaskiya, kuma ba ya iya barin fushi. Ba ya iya hadiye fushi balle ya sallamma wa wanda ya wulakanta shi a cikin mutane. Ba ya kubuta daga giba da keren karya saboda abin da ke gare shi na izza da girman kai suna kange shi daga yin haka.
Babu wata dabi’a abar zargi kuma abar ki face ma’abucin girman kai ya makale mata domin ya tsare izzarsa da girmansa. Saboda haka ne ya zo a cikin Hadisi cewa duk wanda yake da misalin kwayar zarra na girman kai a cikin zuciyarsa ba zai shiga Aljanna ba.
Kuma a cikin wasiyyar Lukman ga dansa ya ce: “Kada ka karkatar da kundukukinka ga mutane, kada ka yi tafiya a cikin kasa kana mai fadin rai. Lallai Allah ba Ya son dukan mai takama, mai alfahari.” (k:31:18)
Ya Ubangiji! Ka tabbatar da imaninmu tabbatar kafaffun duwatsu. Ka datar da mu ga yin ayyuka nagari masu tabbata, Ka nesanta mu daga hanyoyin masu kari (bidi’a). Ka kawar da mu daga wuta, Ka shigar da mu Aljanna mayalwaciya, Ya Mai daukaka darajoji! Domin rahamarKa ya Mafi jin kan masu jin kai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a kan Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya.
Huduba ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mamallakin Ranar Sakamako. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a kan Annabinmu Muhammad wanda aiko shi ya kasance rahama da shiriya ga talikai, da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ya bayin Allah! Mutakkabiri mai dukiya yakan zaci cewa shi an wakilta masa arzikin bayi ne. Kuma shi wani mai girma ne da aka daukaka, wanda ake yi masa biyayya kuma mai yawan kyauta. Shi kuma mutakabbiri matalauci zai riga daga kai alhali shi mai bukatuwa ne zuwa ga abokai da sauran mutane. Mai griman kai yakan yi zaton shi ne yake juya harkokin duniya yake daga madogaran sama. Yakan yi wahamin cewa shi ne ya shimfida filin kasa, shi ke tafiyar da iska ya shimfida kasa ya tabbatar da ita da turaku. Malami mai alfahari yakan yi zaton shi ne mai kira zuwa ga shiriya, shi ne mai tserar da kasa daga illar fasadi. Samari ko matasa masu girman kai, sukan dauka su ne jigogin kasa, su ne wadanda ake ba muhimman al’amuran rayuwar duniya, alhali su gajiyayyu ne ga kowace shiryarwa da gyara da kyautatawa. Magana ta gaskiya lallai mutakabbirai ba su iya gyara komai.
Ya Ubangiji! Ka yi wa mutakabbirai (masu girman kai) da masu ketare iyaka irin abin da Ka yi ga mutanen Annabi Nuhu da Adawa da Samudawa da Fir’auna ma’abucin turaku. “A lokacin da suka mance abin da aka tunatar da su da shi. Sai Muka bude a kansu kofofin komai, har lokacin da suka yi farin ciki da abin da aka ba su, sai Muka kama su kwatsam! Sai ga su tsuru-tsuru an lullube su da azaba. Sai aka yanke bayan wadanda suka yi zalunci (aka halaka su), kuma godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.”
Ya Ubangiji! Muna neman tsari da hasken kudusinKa da girman albarkarKa da daukakar tsarkinKa da albarkar girmanKa daga dukan wata cuta da cutarwa. Kuma daga sharrin masu aukowa a cikin dare da rana na daga aljannu da mutane face mai aukowa da alheri. TsarkakarKa ta tabbata muna godiya gare Ka girmamawa ga girmanKa da karramawa ga karimcinKa da ikirari ga girman AnnabinKa da furuci da kadaicinKa da kuma tsarkake Ka daga abin da kafirai da azzalumai da masu jayayya suke fada, Ka daukaka daga haka daukaka mai girma.
Ya Ubangiji! Ka tserar da mu daga kaskantarwarKa da kuma sharrin bayinKa, Ka doka mana tambarin tsaronKa, Ka sanya mu cikin tsaronKa da kularKa, Ka ba mu alherinKa, ya mafi rahamar masu rahama.