Fitacciyar jarumar finafinan Kannywood Hadiza Gabon ta sake tayar da ƙura, bayan da ta gargaɗi matan da ba su shigar harkar fim ba cewa su guji hakan.
Jarumar wacce ta koma mai shirya tattaunawa a shirinta mai suna Gabon’s Room da take sa wa a tashar You Tube ta yi kira mai kama da gargaɗi da ke nuna cewa ahir ɗin matan da shiga harkar, wanda hakan ya janyo ce-ce-ku-ce a masana’antar da jama’ar gari tare da mayar mata zazzafan martani daga wasu abokan sana’arta.
- Matan shugabannin kasa: Salonsu da tasirinsu
- Sama da mutum 1.8m ne suka yi aikin hajjin bana — Saudiyya
A farkon makon nan ne a shirin nata na Gabon’s Room wanda take hira da jaruman masana’antar da wasu fitattun mutane a wannan karo ta karɓi bakuncin Surayya Aminu, wacce aka fi sani da Rayya ta shirin Kwana Casa’in mai dogon zango na Tashar Arewa24.
Rayya ta tambayi Hadiza shawararta ga su sababbin shiga masana’antar. Ita kuma ta amsa mata da cewa ita yanzu da ta samu kanta a ciki, tana yi mata fatar ta gama lafiya.
Waɗanda kuma shirin fim ke burge su kuma suke son shigowa. To, ahir ɗinsu. Domin rashin alherin sana’ar ya fi alherinta yawa.
“Ku da kuke ciki kun riga kun fara, fatata ita ce yadda kuka soma lafiya Allah Ya sa za ku gama lafiya.
“Amma waɗanda ba su shigo ba suna gida suna tunanin za su shigo, wallahi kada ku shigo,” in ji ta.
“Saboda me za ki ce kada su shigo?” Rayya ta tambaye ta cikin mamaki.
“Saboda disadvantages (rashin amfanin) zama din ya fi advantages (amfani) din yawa,” in ji Hadiza Gabon.
Sannan ta ci-gaba da bayyana mata dalilinta na faɗin haka da kuma fashin baƙin abin da take nufi, domin idan tafiya ta yi nisa kuma mutum ya samu ɗaukaka a sana’ar akwai abubuwa marasa daɗi da ka iya biyowa baya.
Ta ce, “Sai ka kai wata kololowa a daukaka, ba ka yi abu ba, sai a ce ka yi. Za a yanke maka hukunci, za a zage ka, za a ci maka mutunci.
“Za a ci wa iyayenka mutunci, za a ci wa sana’arka mutunci kuma ba ka isa ka yi magana ba. Ko kana da gaskiya ko ba ka da gakiya dole ne ka yi shiru.”
“Idan wani abin alheri zai same ka sai a ce ’yar fim ce, za ka wayi gari kana so za ka yi aure ga maza sun fito za a je a samu mijin a ce me za ka yi da ’yar fim. ’yar iska, ’yar kaza da kaza…” in ji Gabon.
Wannan furuci duk da cewa kalamai ne da ke nuna wallen Kannywood ba sabon abu ne, kuma kalaman nata kamar sauran, sun janyo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen masana’antar har da raddi daga wasu jaruman.
Zaharadden Sani, ɗaya daga cikin jaruman masana’antar a wani sautin murya da ya fitar ya kalubalanci jarumar a kan furucin da ta yi.
Jarumin ya zargi jarumar da zama tamkar kaza ci ki goge bakinki dangane da alheri da kuma ɗaukakar da ta samu a Kannywood, tare da bayyana cewa ba ta yi wa masana’antar adalci ba.
Yana mai cewa kowa ya lalace shi ya so. “…Wato duk macen da ba ta shiga fim ba kada ta shigo, wato mu duka ’yan iska ne?
“Dama sun mayar da kansu ’yan iska, mata da maza ’yan fim nawa ne suka yi aure, ba ga A’isha Tsamiya ba, ta yi aure tana gidan mijinta…Wato tunda ita ta yi kuɗi ta yi mota a daina fim ke nan. Ta zama ’yar jarida, to, ba za a daina fim ba a duniya har a busa kaho,” in ji shi.
Jarumin ya ɗora lalalcewar ’yan fim da tarbiyyarsu da inda suka taso. Yana mai cewa shi bai ga illar sana’ar ba, ko barnar da ke ikirari a cikinta domin shi zai iya sa ’ya’yansa a fim in suna sha’awa.
“Su idan suna abin da tsofaffin jaruman da suke yi da kuma abin da manyan suka gaya musu za su zama haka ne …duk macen da ba ta kama kanta ba ina za ta samu mijin aure, wa zai aure ta?
“Ai, irin waɗannan sun san ba za su auru ba ne. Idan da ta kama kanta da tuni ba ta yi aure ba ne, ’yan matan fim nawa ne suka yi aure, akwai mai auren zuriyar Sarkin Kano ma,” in ji shi.
Martanin na Zaharaddeen shi ma ya janyo ce-ce-ku-ce musamman a shafafuka sada zumunta na Intanet.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka ga beken jarumin kan abin da Hadiza Gabon ta fada shi ne wani Shaihun Malami, Barista Is’hak Adam Is’hak inda a cikin wa’azin ya daki jaki ya kuma daki taiki kan lamarin da kuma dalilan mata ke shiga shirin fim a fahimtarsa.
Ya ce, “Mace ce mijinta ya kasa riƙe ta, ya kore ta da ’ya’ya biyu ko uku, ta rasa abin da za ta yi kuma tana da sura mai kyau, sai kawai ta shiga fim.
“Ta shiga ce da niyyar ta yi sana’a ta samu abin za ta bai wa ’ya’yanta. Ba kuma na ce sana’ar daidai ba ce.
“Amma dai da yawan abin da ke kai su ke nan. Wasu kuma ’ya’yan talakawa ne sun rasa yadda za su yi da rayuwa sai su shiga.
“…. Bayan mutum ya shiga idan ya ga da akwai matsala laifi ne ya fada? A cikin ’yan fim akwai mutanen kirki, akwai na banza, amma kuma mafi yawa cikin mata na ganin abubuwa na rashin kirki har da mazan,” in ji shi.
Ba wannan ne karo na farko da aka samu irin wannan furuci daga ’yan masana’antar ba wanda wasu ke gani tamkar kirari ne a kasuwa bayan mutum ya daɓa wa kansa wuka.
Ko da yake Hadiza Gabon ba ta fito ƙarara ta kama suna ko bayar da misalai ba, amma Abdullahi Amdaz wani jarumi a baya ya taɓa fitowa ya yi wasu bayanai irin waɗannan.