✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gare ku mujirimai (1)

Huduba ta Farko:Hamdala da taslimi. Ka ji tsoron domin tsoron Allah bai shafar zuciyar mutum face ya sadar,Ba wanda ya kashe wani ba ne jarumi…

Huduba ta Farko:
Hamdala da taslimi.
Ka ji tsoron domin tsoron Allah bai shafar zuciyar mutum face ya sadar,
Ba wanda ya kashe wani ba ne jarumi wanda ya ji tsoron Allah ne jarumi.
Ya bayin Allah! Ubangijin Izza da daukaka Yana ba mu labara a cikin LittafinSa kan misalan jama’ar da ta lalace ta kware wajen dagawa da fasadi da girman kai da barna a bayan kasa. Daga cikin misalan wannan al’umma masu fasadi akwai mujirimai.
Mujirimai su ne wadanda Allah Ya ambace su a cikin LittafinSa a wurare da dama Yana ba mu labarin halayensu a duniya da dagawarsu a cikinta da adawarsu ga manhajar Allah da Manzanni da mabiya Manzannin na daga masu da’awa da muminai. “Kuma kamar haka Muka sanya ga kowane Annabi abokan adawa daga mujirimai. Kuma Ubangijinka Ya isa zama mai shiryarwa da taimako.” (Furkan:31) “Sannan Muka aiko a bayansu da Musa da Haruna zuwa ga Fir’auna da mukarrabansa da ayoyinmu amma sai suka yi girman kai, kuma suka kasance mutane masu mujirimanci.” (Yunus:75)
Kuma Alkur’ani ya ba mu labarin Musa (AS) yana siffanta Fir’auna da mutanensa lokacin da suka karyata shi: “Sai ya kira Ubangijinsa cewa, “lallai wadancan (su Fir’auna) mutane ne  mujirimai. (Ad-Dukhan:22).
Duk wanda ya zama karfen kafa ga Annabawa da masu gyara shi mujirimi ne, kuma duk wanda yake adawa da waliyan Allah da muminai shi mujirimi ne. Asalin mujirimi shi ne wanda yake kulla sharri ya yanke alheri. Allah Ya yi ilhamar alheri da sharri ga zuciyar  dan Adam: “(Kuma ina rantsuwa) Da rai da Abin da Ya daidaita ta. Kuma Ya sanya mata (ya yi mata ilhamar) fajircinta da takawarta.” (Asshamsu:7-8).
Allah Madaukaki bai aiko Manzanni ba, kuma bai saukar da Littafi ba, kuma bai ba da da hankali ba, bai ba da fitira da za ta tunatar da bawa kan Ubangijinsa ba, kuma bai kwadaitar kan Aljanna ko ya tsoratar kan wuta ba, kuma bi farlanta ukubobin shari’a ba face domin ya karya zuciyar dan Adam daga aikata mujirimanci!
Ya bayin Allah! Lallai Allah Shi ne Mahaliccin muminai kuma Shi ne Mahaliccin kafirai, Shi ne Mahaliccin mala’iku masu da’a da shaidanu, kuma Ya san a cikin haka akwai fa’idoji da hikimomi masu yawa. Daga ciki har sai gurabun sunayen Allah Madaukaki masu girma sun bayyana. Misali sunan Muntakimu (Mai tsananin kamu) ba zai bayyana ba, sai an samu mujirimin mutum. Haka sunan Algafuru (Mai yawan gafara) ba zai bayyana ba, sai an samu bawa mai tuba wanda ya je ga Ubangijinsa yana fatar rahamarSa da gafararSa. Sunan Alwadudu (Mai nuna soyayya) ba zai bayyana ba, sai an samu bawa mai soyayya domin Allah wanda kuma Allah Yake sonsa.
Hakika Alkur’ani Mai girma ya yi ta bayanin siffofin mujirimai da bayyana hanyoyinsu da manhajarsu da alamominsu domin kada hanyar mujirimai ta cakuda da ta muminai, kada dabi’a da halayen muminai su gauraya da na mujirimai, ta yadda kada ayyukan batattu da mujirimancin mujirimai su zamo suna da hadafi a zatin addinin Allah Madaukaki. Allah Ya yi gaskiya lokacin da Ya ce: “Kuma domin hanyar mujirimai ta bayyana.” Al- An’am:55). Hanyar muminai ita ce alamarsu da tafarkinsu da dabi’unsu, kuma ta yi kusa ta yi kamanceceniya a kowane zamani da kowane wuri. Allah Madaukaki Yana cewa: “Kuma kamar haka Muka sanya a kowace alkarya manyanta su ne mujirimanta, domin su yi makirci a cikinta, kuma ba su yi makirci ba face ga kawunansu amma ba su sani ba.” (Al-An’am:123) Manya su ne madaukaka da ake kira manya ko dattawan kasa, sharri da bala’i ba su fitowa sai ta wurinsu.
Duk wani dagutu ko mai dagawa da ke kashe mutane haka kawai, ko yake raba dubbai da gidajensu, ko yake kwace da lalata dukiyarsu, yake watsa tsoro da firgiji a tsakanin jama’a, yake watsa fasadi a bayan kasa to shi mujirimi ne. Kuma haka yana ta maimaituwa a kowane zamani da kowane wuri. Sai dagutu mujirimi ya rika aikata ayyukan mujirimanci kamar zubar da jini da wargaza zaman jama’a.
Allah Ya buga misali da Fir’auna ga masu dagawa, inda yake bda’awar mallakar kasa da mutane da dukiya da koramu (kamar rijiyoyin maid a albarkatun kasa) sai ya ce: “Ashe ba ni ne mai mulkin Masar ba, kuma wadannn koramu suna gudana a karkashina? Shin ba za ku yi dubi ba?” (Zukhrufi:51). Kai ya ma daukaka kansa inda ya ce: “Ni ne ubangijinku mafi daukaka.”
Duk wanda ya yi zaton haka a zuciyarsa ba zai taba karba nakadi ko muraja’a ko ta’akibi ba. Domin bai ganin kowa sai kansa, shi ne mai girma shi ya san komai, shi ne abin alfahari, shi ne madaukaki, shi ne masanin falsafa, shi ne kwamanda, shi ne shugaba, shi ne abin koyi, shi ne masani, shi ne mai yanke hukunci, shi ne mai huduba, shi ne wanda ba ya kuskure.
Kuma lallai daga cikin alamomin mujirimai akwai kawara da manhajar Allah daga rayuwa. Duk wanda ya cire manhajar Allah daga rayuwa ya yi hukunci da shari’ar da ba ta Allah ba, kuma ya yi ittikadin ba za a iya dabbaka manhajar Allah a rayuwa ba, mujirimi ne. Duk wanda ya cutar da al’umma ya kashe dubbai ya raba dubbai da muhallinsu, saboda ya samu hanyar ci gaba da mulki koda zai rika taka gawarwakin mutanensa masu rauni shi mujirimi ne. Duk wanda ya juya dukiyar al’ummarsa zuwa ga cimma biyan bukatar ci gaba da zama kan kujerarsa da sha’awoyinsa, ya bar talakawa cikin yunwa da rayuwa cikin tsananin sanyi  da talauci da rasa kayan bukatun rayuwa alhali an shimfida wa kasar dimbin dukiya, duk wanda ya aikata haka yana amfani da siyasar nan ta “Ka yunwatar da karenka domin ya yi maka biyayya,” shi mujirimi ne! Kuma da sannun jama’ar kasar za su cinye shi maimakon su yi masa biyayya.
Duk wanda bai ba dan Adam kima, bai san komai ba sai wahalar da duk wanda ya saba wa ra’ayinsa ko ya yi ishara da haka, to shi mujirimi ne!
Mujirimai a cikin Alkur’ani su ne duk wanda ya zamo tushe na aukuwar cuta da sharri. Allah Madaukaki Ya ce: “Face ma’abuta dama. A cikin Aljanna suna tambayar juna. Game da mujirimai. (Suna cewa): Me ya shigar da ku cikin wutar sakar? Sai suka ce: “Ba mu kasance daga cikin masu Sallah ba. Kuma ba mu kasance muna ciyar da miskinai ba. Kuma mun kasance muna kutsawa tare da masu kutsawa. Kuma mun kasance muna karyata Ranar Sakamako. Har mutuwa ta riske mu.” (Mudassir:39- 47).
Sallah misali ne na kowace ibada, amfaninta yana takaita ne a kan ma’abucinta kawai, zakka misali ne na da’a da amfaninta ke kaiwa ga wasu. Don haka duk wanda ya kasance ba ya da alheri a kan kansa to ba zai zamo alheri ga wadanda suke tare da shi ba, zai rusuna ga karya ya zamo tushen sharri da cutarwa don haka ya zama mujirimi.
Daga cikin mujiriman da aka ambata a cikin Littafin Allah akwai mai isgili ga muminai. “Lallai wandanda suka yi mujirimanci sun kasance suna yi wa muminai dariya. Idan suka wuce ta wurinsu sai su yi ta zundensu. Idan kuma suka juya zuwa ga iyalansu, sai su juya suna masu farin ciki. Idan suka gan su sai  su ce, “Lallai wadancan batattu ne.” (Mudaffifin:29-32).
Sunnar Allah a bayan kasa ita ce wadanda suka yi isgili ga Annabawan Allah (AS) suk tuhume su da yin sihiri da karya da hauka, misalansu da magadansu suna nan a kowane zamani, suna tuhumar muminai da masu son gyara da leken asiri da kullalliya da kauyanci da tsanani tsoma baki kan ’yancin jama’a, suna siffanta su da dabbobi.
Hakika mujirimai suna amfani da kafafen watsa labaransu wajen zana hotunan takala domin isgili gare su da amfani da alkalumansu wajen isgilanci da wasa da addinin Allah a fili kiri-kiri suna dariya ga ma’abuta imani.