Assalamu alaikum warahmatullah uwar ’ya’ya. Mun koro bayanai kan yadda za ki dora ’ya’yanki a turba ta kwarai don a samu al’umma mai jin dadin rayuwa a nan duniya, a je Lahira a iske Allah lami lafiya. To yau za mu dasa aya da wasu dabi’un kamar haka:
Ladubban zama da makwabta:
Allah Mahaliccin kowa da komai, Masanin abin da zukata suke kullawa da kwancewa Ya umarci Musulmi da cewa: “Kuma ku bauta wa Allah kada ku hada wani da Shi, kuma ga mahaifa ku yi kyautatawa, kuma (ku kyautata) ga ma’abucin zumunta da marayu da matalauta da makwabci ma’abuncin kusanta da makwabci manisanci da aboki a gefe da dan hanya (matafiyi) da abin da hannuwanku suka mallaka (bayi/barori). Lallai ne Allah ba Ya son wanda ya kasance mai takama mai yawan alfahari.” (Nisa’i: 36).
Idan muka kalli wannan aya kusan ta gama komai game da dangantaka a tsakanin bawa da Ubangiji da tsakanin mutum da mutum. An fara da fadin hakkin Allah a kan bawa, aka dawo kan mafi hakki a kan mutum bayan Allah wato iyaye aka ce a kyautata musu. Daga nan aka zo kan dangi, sai marayu, sai makwabta na kusa sai na nesa sai aboki sai matafiyi. Shin akwai wanda aka rage a cikin abokan hulda?
To amma yanzu muna magana ce kan zamantakewa da makwabta. Makwabci ma’abuncin kusanci shi ne wanda yake kusa da gidanku ko wanda yake dan dangi, makwabci manisanci shi ne wanda yake nesa da gida ko babu dangantaka ta jini. Duk da haka Annabi (SAW) ya kwadaitar a hadisai da dama kan kyautata mu’amala da makwabci da kyautata masa da guje wa musgunawa ko cutar da shi ta kowace hanya. Har ma ya ce: “Jibrilu bai gushe ba yana yi min wasiyya game da makwabci har na zaci cewa lallai zai iya gadarsa.” (Muttafakun alaihi).
Don haka ki koya wa ’ya’yanki mutunta makwabtanku, kada ki kuskura ki nuna musu ba ku shiri da makwabta koda kin samu sabani da su. Domin Hadisin da ya gabata ya nuna kaiwa karshe wajen dangantaka a tsakanin makwabta.
Sannan ki nuna musu illar cutar da makwabtan ko ’ya’yansu. Kuma ki nuna musu amfanin taimakon ’ya’yan makwabtan da iyayensu. Musamman duk lokacin da kuka sauya abinci mai dadi ko kuka samu wani abin marmari ki tunatar da shi kan makwabta, idan aka dafa ki tura yaranku da dan abin da ya samu su kai musu. Wannan zai sa su san muhimmancin makwabtan, kuma soyayya ta kullu a tsakaninsu da ’ya’yan makwabtan. Ba makwabci kyautar abinci ko abin sha, umarni ne na Annabi (SAW) inda ya ce: “Ya Abu Zarrin idan ka dafa nama ka yawaita ruwansa (romo) ka bai wa makwabtanka.” (Muslim).
Kuma ba koyarwar Musulunci ba ce ku take cikinku da abinci alhali kun san makwabtanku suna fama da yunwa, in kuka fahimci ba su da abinci ku tallafa musu gwarwado. Saboda Annabi (SAW) ya ce: “Ba mumini ba ne wanda zai koshi amma makwabcinsa yana fama da yunwa.” (Al-Adabul Mufrad).
Hulda da wadanda ba Musulmi ba
Musulunci addini ne da ke girmama dan Adam ko yaya yake. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma lallai ne Mun girmama ’yan Adam, kuma Muka dauke su a cikin kasa da teku, kuma Muka azurta su daga abubuwa masu dadi, kuma Muka fifita su a kan masu yawa daga wadanda Muka halitta, fifitawa.” (Isra’i: 70). Don haka ya ke uwar ’ya’ya ki nuna wa ’ya’yanki cewa duk mutumin da suka gani koda ba Musulmi ba ne, kada su kurkura su wulakanta shi ko su ci masa mutunci ko su cutar da shi.
Annabi (SAW) ya rayu da mutane mabambanta addini cikin girmamawa da mutuntuwa da kare musu hakki. Lokacin da ya isa Madina musamman ya sa aka tsara tsarin mulki na zamantakewa a tsakanin mabambantan mutanen Madina. Wannan tsarin mulki ko yarjejeniya ta tabbatar da adalci a tsakanin mutane koda sun saba wa Musulmi wajen akida ta yadda aka hana a tilasta wa dayansu shiga Musulunci. Dama Allah Ya ce: “Kuma da Ubangijinka Ya so da wadannda suke a cikin kasa sun yi imani dukkansu gaba daya. Shin kai kana tilasta mutane ne har sai sun kasance masu imani?” (Yunus:99). To tunda mun san Allah bai halicci mutane don su zamo muminai dukkansu ba, abin da ke kanmu mu mu’amalnce kowa cikin adalci da kyautatawa da mutuntawa, kila ta wajen kyautatawa da mutuntawar sai abokan zamanmu da ba Musulmi ba su yi sha’awar addinin. Kada ki bari danki ya zamo mai zagin wadanda ba addininku daya ba, ko mai cutar da su, ko mai zaluntarsu ko cin fukarsu, kamar ya rika ce musu arnan banza ko kafiran banza da zarar sun samu sabani ko rashin fahimta.
Kada ki yarda danki ko ’yarki ta cutar da dan wadanda ba Musulmi ba da kuke zaune tare ko wata harka ta hada ku. A’a ki koya musu cewa su yi abin da zai burge su har su yi sha’awar shiga Musulunci. Allah Ya yi umarni ga Annabi (SAW) cewa idan mushiriki ya nemi ya yi makwabtaka da shi, to ya amince da makwabtakar har mushirikin ya ji kalmomin Allah. Wato ya ji kalmomin Allah a furuci kuma ya ga kalmomin Allah a aikace ta wajen kyawawan halaye da dabi’un da Musulunci ya zo da su.
Wadanda ba Musulmi ba suna da hakki Musulmi su yi musu adalci kuma su kyautata musu matukar ba suna yakar Musulmin ba ne a lokacin. Domin Allah Madaukaki Ya ce: “Allah ba Ya hana ku daga wadanda ba su yake ku ba saboda addini kuma ba su fitar da ku ba daga gidajenku, ga ku kyautata musu kuma ku yi musu adalci. Lallai Allah Yana son masu adalci.” (Mumtahanna: 8).
Shin idan muka kiyaye ’yan abubuwan da muka gabatar a wannan shafi a ’yan makonnin nan, ya ke uwar ’ya’ya! Ba ki jin za a samu sauyi a yanayin zamantakerwar al’ummarmu? Don haka ya kamata ki sani gyaruwar al’umma yana hannunki ne, idan aka ga mutane sun lalace to ki sani daga gare ki ne a matsayinki ta uwa. Muna fata dan wannan rubutu zai zamo kaimi gare ki wajen sake fasalin yadda kike tafiyar da gidanki.