Aminicin Allah da rahamarSa su tabbata gare ki, ya ke uwar ’ya’ya! Bayan haka na san kina sane da cewa a matsayinki ta uwa ke ce ginshiki mafi girma na samar da al’umma tagari. Idan ba ki kintsa gida da mutanen cikinsa ba, wannan rashin kintsi zai bayyana a kofar gida zuwa makwabta zuwa unguwa zuwa gari zuwa kasa baki daya. Ashe ke nan samuwar al’umma tagari mai kyawawan dabi’u yana wuyanki ne fiye da kowa. Kada ki manta kintsuwarki ce kintsuwar mijinki, kintsuwarki ce kintsuwar ’ya’yanki haka lamarin zai tafi har kan jikokinki.
A matsayinki ta uwa Musulma ke ce za ki gina abin da Annabi Muhammad (SAW) ya fi kira a kansa, wato kyawawan dabi’u, wadanda ma a wani wuri ya takaita da’awarsa da su inda yake cewa: “Abin sani an aiko ni ne don in ciccika kyawawan halaye.” (Ahmad ya ruwaito).
Ya ke uwar ’ya’ya! Ki sani Annabi (SAW) ya bayyana cewa ana gane alherin mutum ne ta hanyar lura da kyawawan halayensa. Shi ya sa Annabi (SAW) yake cewa: “Mafi cikar imani a cikin muminai shi ne wanda ya fi su kyawawan halaye.” (Ahmad da Tirmizi suka ruwaito).
Ibn Kayyim (Allah Ya yi masa rahama) ya ce, “Addini gaba dayansa kyawawan halaye da dabi’u ne. Abin da ya karu gare ka na kyan hali, sai ya kara maka kyan addini.” (Midarajus Salikina:2/307).
Tunda yanzu mun san kyawawan halaye su ne mutum su ne kuma addini, kuma ke uwa ke ce makarantar raino da taitayar mutum ya zamo mai kyawawan halaye, to wadanne halaye da dabi’u Musulunci ya nemi ki dabi’antu da su kuma ki koyar da ’ya’yanki?
Ya ke uwar ’ya’ya! Ki sani daga cikin dabi’u da kyawawan halayen da suka wajaba ki siffantu da su kuma ki koyar da ’ya’yanki akwai:
1. Gaskiya:
Gaskiya ita ce harsashin da aka gina addini a kai, kuma ita ce ginshikin tabbatar da yakini, sannan ita ce darajar da take bin darajar annabta a baya, Annabta kuma ita ce daraja ta kololuwa a duniya. Ki sani lallai Allah Madaukaki Ya umarci bayinSa kan su lizimci bin tafarkin masu gaskiya. Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa kuma ku kasance tare da masu gaskiya.” (Tauba:119). Kuma Madaukaki Ya ce, gaskiya tana gadar da takawa inda Ya ce: “Wanda ya zo da gaskiya kuma ya gaskata ta, wadannan su ne masu takawa.” (Zumar: 33). Sannan Ya bayyana cewa a Ranar Alkiyama babu abin da zai amfani bawa face gaskiya, inda Ya ce: “Wannan ne ranar da gaskiyar masu gaskiya take amfanarsu. Suna da Aljanna wadanda koramu suke gudana daga karkashinsu, suna masu dawwama a cikinta har abada. Allah Ya yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Wannan ne babban rabo mai girma.” (Ma’ida:119).
Annabi (SAW) ya yi umarni a siffantu da gaskiya a yi aiki da gaskiya a tsayu a kan gaskiya. Kuma ya yi hani kan akasinta (wato karya), ya nuna mugun karshen mai bi ko aiki da sabanin gaskiya. Saurari abin da yake fadi: “Ina horonku da (yi ko bin) gaskiya domin gaskiya tana shiryarwa zuwa ga da’a (ayyukan kwarai) kuma da’a tana shiryarwa zuwa ga gidan Aljanna. Mutum ba zai gushe ba yana yin gaskiya yana aikata gaskiya har sai an rubuta shi a wurin Allah a matsayin mai yawan gaskiya. Kuma ina gargadinku kan ku guji karya. Domin karya tana jan mutum zuwa ga fajirci. Kuma lallai ne fajirci yana jan mutum zuwa ga wuta. Mutum ba zai gushe ba yana karya yana aikata karya face an rubuta shi a wurin Allah a matsayin mai yawan karya!” (Buhari da Muslim).
Ya uwar ’ya’ya! Kina son mutanen gidanki su tsira gobe Kiyama? Idan eh ne, to ki dora mijinki da ’ya’yanki da sauran wadanda suke karkashin kularki a kan aikata gaskiya da rike gaskiya da tsayuwa a kan gaskiya. Kada ki yarda ki dora su a kan karya da aikata karya da son yin karya a komai nasu.
Babu alfanu ko kadan mutum ya dora rayuwarsa ta kasance a kan karya ko ya zamo mai furta karya ko mai aikata karya don kawai wannan ’yar rayuwar duniya takaitacciya.
Ki sani ya ke uwar ’ya’ya! Gaskiya tana da riba mai yawa. Daga cikin ribobin gaskiya akwai gadar da gidan Aljanna kamar yadda muka gani a ayoyi da hadisan da suka gabata. Na biyu tana haifar da natsuwa a zuciya ta hutar da rai daga damuwa da kunci. Kan haka ne Annabi (SAW) yake cewa: “Lallai ne gaskiya natsuwa ce, karya kuma na haifar da shakku.” (Tirmizi). Sannan gaskiya wata hanya ce ta samun takawa wato tsoron Allah da kiyaye dokokinSa kamar yadda muka gani a ayar da ta gabata.
Sannan gaskiya za ta sanya Allah Ya so ka, kuma Ya sa mutane su so ka. Kuma gaskiya takan zamo sila na tsira da kubutar bawa daga dukkan abubuwan da suke jawo hallaka.
Uwar ’ya’ya kada ki manta yin gaskiya da tsayawa kan gaskiya da fadin gaskiya suna jawo albarka a rayuwa.
Don haka a matsayinki na silar samar da al’umma tagari akwai bukatar ki dora iyalan gidanki a kan aiki da gaskiya da bayyana gaskiya da tsayuwa kan gaskiya. Ki sani gaskiya tana kasancewa ce a cikin komai na daga maganganu da ayyuka da halaye da niyya da kudiri.
Kada ki manta idan aka ga yaran gidanki ba masu gaskiya ba ne, ke za a fara tuhuma da gazawa.
Sai mako na gaba in Allah Ya kai mu za mu tabo wani halin da ake so ki koyar da ’ya’yanki.