Hadimin Shugaba Buhari kan yada labarai Garba Shehu ya nemi afuwar ’yan Najeriya kan cewar da ya yi dalibai 10 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a makarantar GSSS Kankara.
Garba Shehu ya bayar da hakurin ne a bayan ’yan bindiga sun sako yara 344 ’yan makarantar, sabanin adadin da ya bayar, wanda ya ce ya samu ne daga mutane ne da ya kamata sun san ainihin halin da ake ciki.
- Aisha Buhari ba ta ce komai kan Daliban Kanakara ba
- Yadda aka ceto daliban Kankara a Dajin Zamfara
- Yadda muka sasanta aka sako Daliban Kankara ba biyan kudin fansa
- Yadda na rayu a kurukuku kwana 5 —Sanata Ndume
“Ina ba da hakuri kan kuskuren da aka samu a bayanin da na yi cewa dalibai 10 ne aka sace a Makarantar Sakandaren Kankara
“Na samu bayanin ne daga mutanen da ya kamata su san hakikanin abin da ke faruwa amma sai ya saba da gaskiyan lamarin a lokacin.
“Ina rokon a fahimci cewa ba na yi hakan ba ne da nufin nuna rashin tsananin lamarin. Don Allah ina rokon gafara….”
Idan ba a manta ba an yi ta samun bayanai masu karo da juna ka adadin daliban da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Sai dai adadin da Garba Shehu ya bayar na mutum 10 shi ne mafi karanci, yayin da Gwamantin Jihar Katsina ta ce dalibai 333 ne kafin daga baya ta ce an gano wasu karin daliban.
A jawabin da aka ji a wani bidiyon da ’yan bindigar suka yi kuma sun yi da’awar cewa yara 520 ne a hannunsu a lokacin.
A wani rahoto da Aminiya ta yi kuma, wakilinmu ya ce rajistar makarantar ta nuna yara 668 ne ba a gani ba.
Amma bayan an tattauna an sako yaran, sai aka iske su 344 ne, kamar yadda hukumomi da wasu daga cikin daliban da aka tattauna da su suka tabbatar.
Daya daga cikin yaran da aka zanta da shi ya tabbatar wa ’yan jarida cewa babu wanda ya mutu da cikinsu a wurin ’yan bindigar ko suka rike.