Tsohon dan kwallon kafar Super Eagles Garba Lawal ya zama kocin kulob din Kaduna United da ke Kaduna.
A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta hannun jami’in hulda da jama’a na Ma’aikatar Matasa da Wasanni Zakari Haruna Isa ta ce, gwamnatin jihar ta dauki Garba Lawal ne a matsayin sabon Manajan kulob din saboda gogewarsa a harkar kwallo. Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin jihar ta yi imani Garba Lawal yana da basirar da zai daga martabar kulob din a gasar rukuni-rukunin Premier na kasa da sauran wasanni.
“Gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da nada Garba Lawal a matsayin sabon Manajan kulob din Kaduna United don haka an bukaci ya karbi ragamar shugabanci daga tsohon Manajan kulob din Alhaji Mansur Jibo ba tare da bata lokaci ba”, inji sanarwar.
Garba Lawal ya yi wasan kwallo a kulob da dama a ciki da wajen Najeriya. Yana daga cikin ’yan kwallon da suka lashe lambar Zinare a gasar Olamfik a shekarar 1996 kuma ya halarci gasar cin kofin Afirka sau hudu watau a shekarar 2000 da 2002 da 2004 da kuma a 2006. Haka kuma ya halarci gasar cin kofin duniya a shekarar 1998 da ya gudana a Faransa.
Garba Lawal ya zama kocin Kaduna United
Tsohon dan kwallon kafar Super Eagles Garba Lawal ya zama kocin kulob din Kaduna United da ke Kaduna.A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar…
