✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gara sana’a duk kankantarta da yin bara – Ibrahim Makaho

Malam Ibrahim Ahmad Makaho dan garin Albasu da ke Jihar Kano ne mai sana’ar sakar furannin da ake yi domin kawata daki. A zantawarsa da…

Malam Ibrahim Ahmad Makaho dan garin Albasu da ke Jihar Kano ne mai sana’ar sakar furannin da ake yi domin kawata daki. A zantawarsa da Aminiya ya ce duk da kasancewarsa makaho ba ya da ra’ayin yin bara wanda hakan ya sa shi ya kama sana’a:

 

Ga shi na ga kana da matsalar gani amma kuma kana sana’ar saka gidan fulawa na roba. Ko za ka fada mana lokacin da ka fara wannan sana’a?

Na kai shekara uku da fara wannan sana’a. Kuma da girmana na koyi sana’ar. A Jihar Nasarawa na koyi wannan sana’a ta yin gidan ajiye furanni na roba (Flower base)  ban da wannan ma ina yin irin kwalin saka takardar goge hannu (tissue paper).

Idan ka dubi cikin hotunan da ke gabana za ka ga abubuwan da nake yi. Ina kuma saka jakunkunan mata, amma na fi yin wannan gidan saka furanni na roba saboda an fi sayensu.

 

Nawa kake sayar da kowane daya?

Shi wannan karamin idan da furensa a ciki ina sayar da shi Naira 5,000 amma idan mutum ba ya so da furen sai in sayar masa Naira 4,000. Shi kuma dogon idan mutum yana sonsa da furen Naira 7,000 in babu furen Naira 6,000. Kuma ina yin su manya da kanana.

 

Ka yi karatun boko ne?

A’a na dai yi karatun allo amma ban yi na boko ba.

A nan yankin namu idan mutum ya tsinci kansa da nakasa sai a ga yana bara amma kai kana sana’a, mai ya sa haka?

Bara wani lokaci tana zama dole, amma dama ni can tun farko ba ni da ra’ayin bara, domin kafin in fara wannan sana’a ina yin sana’ar sayen wayar hannu  ina mayarwa. Kuma da Allah Ya taimake ni na samu wannan sai na ajiye wancan sana’ar na rike wannan domin wannan ya fi min gaskiya. Amma ni dama tun farko ba ni da ra’ayin yin bara.

 

Ke nan wannan sana’a sa-kai ka yi ka koye ta?

Eh, sa kai ne kawai na yi gaskiya

 

Yaya batun alheri daga wajen jama’a ana samu?

Eh, to ana dan samu sai dai ba yadda ake so ba, sai dai dama na fi son a sayi kayan nawa wanda kuma zai taimaka min idan yana da hali yana iya taimaka min. Amma dai ba a cika samu sosai ba. Akwai dai wani mutum da ya taba yi min wani taimako wanda da farko da ina cin bashi ne in yi aikin, amma tunda ya taimake ni sai na samu dan jari na ci gaba da yi. Ba dai jari ba ne mai yawa amma dai ya taimaka min.

 

Yaya batun iyali?

Ina da iyali kwarai da gaske domin ina da mace daya da ’ya’ya uku a yanzu haka.

 

A cikin shekara uku da koyon wannan sana’a taka ka samu alheri kuwa?

To, gaskiya dai an samu tunda a cikinsa nake ci da sha da ciyar da iyalina. Shi ne alherin da zan ce na samu.

 

Wane jan hankali za ka yi ga matasa na su kauce wa zaman banza su kama sana’a?

Gaskiya mutane ya kamata koda ba irin wannan sana’a tawa  za su yi ba, su samu wata sana’a, domin tana da amfani. Koyaushe a ce ba ka ake yi, gara a ce kai ne ke bayarwa. Mutane ya kamata su samu sana’a komai kankantarta. Kada mutum ya ce sai ya ga kudi a hannunsa tukunna. A hankali za ka samu kudin sannan wata sana’ar da kake yi za ta janyo hankalinsa har ya dauka ya taimaka maka.