Manyan garuruwan Hausawa ana yi musu ganuwa ko badala wadda ake katange su da ita domin tsare gari daga harin abokan gaba. Kuma bayan an gina ganuwa sai a yi musu kofofin shiga cikin garuruwan domin kula da harkar tsaro. Wannan abu ne da ya zama al’ada a manyan biranen Hausawa da alkaryunsu. Wannan ya sa Aminiya ta waiwayi birnin Zariya domin zakulo tarihin ganuwar da ta kewaye garin da kuma kofofin da suke tare da ita.
Birnin Zariya ba a bar shi a baya ba Ganuwar Zariya ita ce kantagar da ta kewaye birnin Zariya. An gina wannan ganuwa ce domin samar da kariya ga jama’ar birnin Zariya daga hare-haren mayaƙa da miyagun dabbobi kamar yadda yake a sauran birane. Suleiman (2007), ya ruwaito cewa an gina wannan ganuwa ce a cikin ƙarni na 15.
Wannan ganuwa ta Zariya, sabuntawa ce kan asalin ganuwar da sarakunan Haɓe suka gina. Suleiman (2007), ya kawo cewa harin da Sarkin Kano Kanajeji (c. 1390 – 1410) da kuma buƙatar da ke akwai na haɗuwar jama’a waje guda domin bunƙasar tattalin arziƙi da inganta yanayin tsaro da sauransu, shi ya wajabta wa jama’ar Zariya sake sabunta ginin ganuwar da ma canja wa fadar masarautar sheƙa zuwa wurin da take a yau wanda ake kira Zariya.
Jama’ar birnin Zariya su suka haɗu suka aiwatar da wannan aiki na gini tare da la’akari da bayar da gudunmawa a fannin da ya dace. Misali, maƙera su ke samar da kayan aiki irin su fartanya, garma, sangwami, magirbi, da sauransu. Magina su ke da alhakin binciko gurbin da za a yi gini, tsara abubuwan da za a yi amfani da su wajen ginin, aiwatar da ginin da kuma tattalinsa. Masassaƙa su ke sassaƙa katakon da ake amfani da shi wajen yin ƙyamare da sauran katakayen da ake buƙata wajen gini, maƙaɗa su suke zaburar da jama’a, haka nan sauran jama’a duk sun bayar da gudunmawa kama daga masu dafa abinci, masu ɗauko ruwa, masu ɗebo ƙasa, masu kwaɓa da sauransu. A haka aka gina wannan ganuwa kamar yadda ya zo a cikin rubutun Suleiman a shekarar (2007).
Bayan kammala ganuwa sai kuma kofofin da ke makale a jikin ganuwar wadanda ake kulle su domin harkar tsaro ga sunaye da kuma kadan daga tarihin kowace kofa a birnin Zariya:
Kofar Kona
Kofar Gayan
Kofar Kuyambana
Kofar Doka
Kofar Bai
Kofar Galadima
Kofar Matarkwasa
Kofar Jatau
A nemi Jaridar AMINIYA don samun cikakken rahoton.