✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gani Ya Kori Ji: Hotunan wasu abubuwan da suka faru a wannan mako

Wani bene mai hawa uku ya rushe a kan titin Unity da ke Kasuwar Kantin Kwari a Jihar Kano.

Gani Ya Kori Ji na Aminiya ya tattaro muku hotunan wasu abubuwan da suka faru a wannan mako da muke bankwana da shi domin kayatar da ku.

Mutane a Biirnin Tarayya na turuwar duba kanun labarun jaridu a ranar Laraba domin sani halin da kasa ke ciki a unguwar Wuse II.
Hoto: Onyekachukwu Obi

 

Tsohon Shuagaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan yayin da ya je ofishin Hukumar Kula da Hadurra ta Kasa domin sabunta lasisinsa na tuki.

 

Yadda wata tankar mai ta kone kurmus a safiyar yau Alhamis a kan gadar ‘Dan Magaji da ke Wusasa a hanyar Kaduna zuwa Kano. Hadarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku tare da asarar dukiya mai yawa.    Hoto: Aliyu Babankarfi Zariya.

 

Yadda Buhari ya danka wa Tinubu tutar jam’iyyar APC bayan lashe zaben fid da gwani da ya yi wanda a aka gudanar a Abuja. Hoto: Buhari Sallau

 

Osinbajo da Tinubu na gaisawa a filin taron Eagle Square bayan kammala zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar, ranar takwas ga watan Yuni, 2022.
Hoto: Buhari Sallau

 

Shugaba Muhammadu Buhari da maidakinsa A’isha a wurin Babban Taron APC na Kasa don fitar da dan takarar Shugaban Kasa ranar Talata.
Hoto: Buhari Sallau
Wani bene mai hawa uku ke nan da ya rushe, benen na kan titin Unity da ke Kasuwar Kantin Kwari ta Jihar Kano.
Hoto: Freedom Radio Nigeria