✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gangankon gwangwanin garewanin gahawa

  Mai shayin Haurobiyawa Shi ke tuttule tulun ruwa Ya a za sanwa Murhu yai ta tafarfasa garwa   Mun kwankwadi ruwan bunu Asirin magabta…

 

Mai shayin Haurobiyawa

Shi ke tuttule tulun ruwa

Ya a za sanwa

Murhu yai ta tafarfasa garwa

 

Mun kwankwadi ruwan bunu

Asirin magabta ya tonu

Sun hana kasa ta ginu

Komai sun sa hannu

Jama’a na ta maganganu

 

Shan koko bukatar rai

Kandamar kunu ma sarai

Surbar shayi sai dankwarai

Wa-ka-ci-ka-ta-shin wasarairai

Ban da tsokanar sakarai

 

Kun ji ta’adar Larabawa

Turka-turkar Turawa

Tattakin takun Turkawa

Majigin maganadisun Mekzikawa

Artabun arangamar Arewatawa

 

Kowa dai ya gyara

Sai shirin ya zam sharbar gara

Mu tattaru kowa ya hallara

Mu daina kwado da dara

Kayan shaye-shaye su bar shuhura

 

Haure-hauren hauragiya

Hargagin hatsaniya

Hayagagar hawainiya

Hautsinin hayya-hayya

Hatsabibancin hatsabibiya

 

Al’umma

Ai fafutikar makoma

Ai aiki kasa da sama

A tattaru kowa ya kama

A yanayin nan ba zama

 

Garmahon Garbatin gidan Shehi

Girma-girma ganin gashi

Balati ta sha washi

Batun aiki ba fashi

Gwamnati tai tsayin tashi

 

Ana ta sukar mashi

Mahukunta sun yi yaushi

Haurobiyawa na biyar bashi

An harzukasu sui ta fushi

Maganganunsu iwa Turancin Faranshi

 

Azargagiyar zargi

Wai Baba yai magagi

Ko ya shige sagagi

Garbati yai firgigi

Ya ce Baba ba wargi

 

Wannan ne wa’adin karkare zango

A kwanshi gara da zago

Ai kidin gangunan bahago

Mu ga takun amarsu ta ango

Har an fara duba agogo

 

Kasa ko’ina a hango

Kayayyaki dibge a shago

Wasu ma sun lafke a kango

Ina gizo-gizon dakin gwaggo

Bar dage kafar farin dango

 

A zaburar da al’umma

Kowa yai kaimin karin himma

Ai kwadon rama

Ai maganin rama

Sai a samu makama

 

A sake sabon salo

An dai yi jimirin kallo

An ga masu dukan kwallo

Ga masu kwankwadar ruwan jallo

Da masu yi wa jama’a gwalo

 

Baban-burin-huriyya

Kai tarairayar tariya

Bin kadin lamuran zirya

Ka watsar da kiren karya

Batun ingarman karfe muke a farfajiya

Bayan dawowar Baban-burin-huriyya daga taron tula tattali tuli-tuli na tsurkun tsakiyar tsukukun Gabashin duniya da Arewacin Ifirikiyya, Haurobiyawa sun jefa azargagiyar zargi kan cewa ko Baba ya je jika makoshi ne har ya yi SHELAR SHATALE-TALEN SHANTAKEWAR SHAN SHAYI? Ganin irin martanin da na yi wa masu kulla-kullar zarge-zargen zaren afatati, sai wasu ma ke son su jefa irin wannan zarge-zargen kan cewa ko dai Direban allin makaratar Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya ne GARBATIN GIDAN SHEHI, marikin garmahon gangunan gunjin Baba?

Da har zan ce ai ba ni ba ne, sai kawai na ji Garbatin gidan Shehi na ta baza batutuwa ta cikin garmahonsa, cewa Baba ba ya na-kasa, ballantana a kasa, a kwashi kashi, musamman in yana bakin dagar dumuiniyar ayyukan tarairayar Haurobiyawa. Hakika na gamsu da wannan amsa, amma yaya za mu yi da masu yi wa Baba lakabin YAWALE, ko dai suna nufin mai yawan yawon walle-walle; ga shi ya yi  shatale-talen shan shayin Larabawa;daga nan ya yi zirya zir zuwa birgimar Birtaniya; daga can zai yi ruju’i ko sai wata nahiyar sararin samamen duniya?

Ko ma dai wadanne irin tsokale-tsokalen tsangwamar tsugudidi tsigarewa za a yi ta yi, na san cewa, ‘zamanin mulkin mulaka’un Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, Shugaban Gudun-loko da Jona-tantin mulki, har YAWON-WUNI-WUNI ya jefa masu fuka-fukin tashi,’ inda suka ta cike-ciken caccakar shafukan laluben jari a mashakatar lilo da tsallake-tsallake. Wasu sun dace, sun dafe wasu kuwa na-mujiya ya kafe, tawayar rayuwa ta kyafe su.

Shi ma dai Baba ai bai yi kasa a gwiwa ba, domin ya bullo da AIKIN FAWA, ka da dai a ce an tura masu fuka-fukin tashi garin FAWWA da ke karkashin masarautar birnin Dikko su yi dakon dako. A’a, an dai bullo da dabarbarun laluben na-koko a cikin kowane loko na kasar Haurobiya da zimmar kawar da zaman kashe fatari da gararambar watangaririya mai hadari.

Akwai dimbin alfanun da Baban-burin-huriyya ya lalubo a balaguronsa, musamman lokacin da ya yi shatale-talen shantakewar shan shayin Larabawa, sannan aka kara da birgimar Birtaniyawa. Lamarin dai na bukatar gwagwiyar goribar garhamahon gurmin garayar Garbatin gidan Shehi. Saboda haka lallai a kwankwadi madin modar gahawa.

Gangankon gwangwanin garewanin gahawa na bukatar gangamin gamayyar gwagwagwar gama-garin al’umma don raba shayin da kowa zai kwankwada ya yi hani’an, tun da mun fasko cewa, ‘Sawun-diyyar Larabawa na shirin kafa katafariyar matankadar tunkuza a Haurobiya, ta yadda watakila a dakile azarbabiyar masu ziryar safarar TURAR-MOLO da KOKINO da sauran nau’ukan shaye-shaye da romon birkita kwakwalwar al’umma. Kai ga ma kokarin kasar Katar ya kayatar.

Uwa-uba, a farfajiyar koyon watsattsake da falle shafukan mujallu da makalu da jaridu da wagagen littattafai, mun yi darasin MAHANGAR MAKEKEIYAR MAKARANTAR MAMA, al’amarin da muka ta’allaka da hadin gwiwar Mama da ‘’yan kayataciyar kasar Katar, har ta hada hannu da mutanen Sudan da suka dare a sirdi sadidan. Wannan ne ya sanya Direban allin makarantar nan bai saduda ba, wajen ganin ya tallafa wa Mama ta kafa Babbar bukkar bobon bokokon Baban-burin-huriyya.

Lallai a sake sabon salo, domin an dai yi jimirin kallo, inda tuni aka fasko masu dukan kwallo da masu kwankwadar ruwan jallo; wasu ma suna yi wa jama’a gwalo; ta cikin kurtun magana kawai sai ka ji masu karatun ALLO, suna ta wataya tamkar masu baza bindin bezar TALO-TALO, sai su ce HALO ALALO!

Sannan  fadin kasa ko’ina a hango irin kayayyakin da ke dibge a shago, don wasu ma sun lafke a kango dabaibaye da yanar gizo-gizon dakin gwaggo, sun ki daina dage kafar farin dango. Saboda haka sai a zaburar da al’umma, kowa ya yi kaimin karin himma. A zo  a yi kwadon rama don  maganin rama, ta yadda za a samu makama.

’Yan makaranta mu nusar da Baban-burin-huriyya bukatar kara tarairayar tariya da bin kadin lamuran zirya, sai ya watsar da kiren karya, don batun ingarman karfe muke a farfajiya

Haurobiyawa mu yi wa kanmu masalaha, mu kiyayi harkalla da hakilon shiga wahala, don haka sai a kula ka da a zubar da kwalla.  In mun kiyaye, za  mu ji dadin dararaku hahaha!